Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
Shugabar ƙungiyar Wayar da Kan Al’ummar Nijeriya don ganin ‘An yi komai daidai’ (DTRT) ta ƙasa Hon. Mahalia Aisha Ahmad Fategi, tsohuwar kwamishiniyyar al’amuran kula da ƙananan hukumomin da masarautu ta Jihar kwara, ta bayyana cewa wajibi ne yanzu matasa su koyi sana’o’i, musamman sana’o’i da suka shafi kimiyya da fasaha.
Ta ce, yanzu su ne abubuwan da ake yayi kuma su ne hanyoyin bunƙasar tattalin arziƙi na ƙashin kanka da al’ummarka, da ƙasarka, dama duniya bakiɗaya.
Hon. Fategi ta bayyana haka ne a wajen taron nuna fasahar da ƙere-ƙeren matasa, da hukumar UNESCO da haɗin gwiwar cibiyar koyar da sana’o’in zamani ta Gwamnatin Kano da ake kira da ALIKO DANGOTE ULTRA MODERN SKILLS ACQUISITION CENTER (ADUMSAC), ƙarƙashin shugabancin Hon. Alkassim Wudil wanda aka gabatar a harabar cibiyar a ranar Litinin ɗin nan da ta gabata.
Haka kuma ta ƙara da cewa duk da ƙoƙarin gwamnatin Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf wajan bunƙasa rayuwar matasa da sauran al’ummar kano ta wacce fuska kamar lafiya noma ilimi kasuwanci, sana’o’i, da sauran su to amma albarkar ta yawan jama’a musamman matasa gwamnatin Kano ba za ta iyya ɗaukar nawun matasa aiki gabaɗaya ba, don haka akwai buƙatar inganta irin waɗannan sana’o’i don amfanin matasa wanda zai kawo bunƙasar tattalin arziƙi a Nijeriya haka ita ma kanta Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu, ba za ta iya bawa kowa aiki a Nijeriya ba, Mafuta kawai a rungumi irin waɗannan hanyoyi na bunƙasa ilimin fasaha da duniya ke yayi a yau.
A ƙarshe Hon. Mahalia Aisha Ahmad Fategi, wacce ita ce ta kafa ƙungiya wayar da kan jama’a ta komai a yi daidai cikin tsari, kuma shugabar ƙungiyar ya yaba wa Gwamnatin Kano kan wannan haɗin gwiwa na shirya wannan taro na ranar buƙasa fasahar yara da matasa da kuma sana’o’i da hukumar kula da yara ta Majalisar ɗinkin Duniya ta UNESCO da haɗin gwiwar cibiyar koyar da sana’o’in zamani ta Kano ADUMSAC ta shirya a wannan jiha ta Kano.
