Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Nijeriya (MACBAN), Baba Usman Ngelzarma, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa matsugunan makiyaya a duk faɗin ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa, irin waɗannan matsugunan za su ƙara haɓaka ayyukan kiwon dabbobi, da inganta tsaro, da kuma samar da ɗimbin ƙarfin tattalin arzikin da ake samu a fannin kiwo a Nijeriya.
Da yake magana a ranar Laraba, game da samar da sabuwar ma’aikatar kiwon dabbobi da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta yi, Ngelzarma ya jaddada cewa magance aalubalen da makiyaya ke fuskanta na da matuaar muhimmanci wajen magance matsalar rashin tsaro da ake dangantawa da ayyukansu.
Ya bayyana buƙatar tattara bayanai kan filayen kiwo, wuraren ruwa, kasuwannin dabbobi, da adadin makiyaya da shanu a Nijeriya.
A cewarsa, irin waɗannan bayanai za su taimaka wa gwamnati wajen samar da manufofin da suka dace da haƙiƙanin lamarin.
“Domin ƙarfafa tsaro da ci gaba, muna buaatar ƙidayar dabbobi. ƙididdigar ƙarshe a wannan fanni an yi ta ne tun a shekarar 1991. Idan ba tare da ingantattun bayanai na zamani ba, ba zai yuwu ba, inji Ngelzarma.
“Ta hanyar tsugunar da makiyaya a wuraren da aka keɓe, za mu iya tabbatar da lafiyar dabbobi, waɗanda za su samar da madara da nama. Matsugunan za su kuma kare makiyaya da dabbobinsu daga ɓarayi da sauran barazana a yayin kiwo,” inji shi.
Ngelzarma ya jaddada cewa, tsarin da aka tsara na kiwon lafiya zai iya samar da guraben ayyukan yi, musamman a yankunan karkara.
Ya ba da misali da ayyukan yi ga likitocin dabbobi, masana kiwon dabbobi, da ma’aikatan noman ciyawa, madara, da sarrafa nama.
Ya kuma ƙara da cewa, a halin yanzu Nijeriya na kashe dala biliyan 2 a duk shekara wajen shigo da kayayyakin kiwo daga ƙasashen waje, lamarin da za a iya sauya shi ta hanyar saka hannun jari a cikin gida.
“Waɗannan al’amura gaba ɗaya ba kawai zai inganta rayuwar makiyaya ba ne, amma zai samar da masana’antu masu inganci da za su iya bunƙasa tattalin arziki da rage dogaro da shigo da kaya daga ƙasashen waje.
“Haɓaka fannin kiwo ba kawai zai haɓaka kiwon dabbobi don nama ba ne, har ma da sanya Nijeriya ta fitar da madara zuwa ƙetare, tare da samun musanya mai kima daga ƙetare,” in ji shi.
Shugaban na Miyetti Allah ya yi kira da a ƙara wayar da kan makiyayan domin gudanar da ayyukansu a cikin tsarin kiwon dabbobi na zamani.
Ya yi imanin cewa irin wannan gangamin wayar da kan jama’a zai taimaka wa makiyaya su yi daidai da manufofin gwamnati da nufin inganta jin daɗinsu da shigar da su cikin ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
“Ya kamata a faɗakar da makiyayanmu sanin alfanun waɗannan manufofin. ɓangaren kiwon dabbobi da ke da kuɗaɗe mai kyau na iya canja rayuwarsu tare da ba da gudunmawa ga ci gaban ƙasa,” in ji Ngelzarma.
Burin ƙungiyar MACBAN mai fafutukar kare haƙƙin jama’a da haɗa kai, ita ce ciyar da rayuwar Fulani makiyaya gaba a Najeriya, wanda aka kafa a farkon shekarun 1970, mai hedikwata a Kaduna. A cikin 1979, an kafa ta bisa ƙa’ida, kuma a cikin 1987, an fi saninta sosai a matsayin ƙungiyar bayar da shawarwari.
