Dakarun adawa sun hamɓarar da Shugaba Al-Assad na Siriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƴan ɓangaren adawa na ƙasar Siriya sun ce mayaƙansu sun yi nasarar karɓe Damascus, kuma Shugaba Bashar Al-Assad ya tsere daga ƙasar.

Kwamandan tawagar Tahrir Al-sham, Abu Muhammad Al-julani ya ce baki ɗaya ma’aikatun ƙasar za su kasance ne a ƙarƙashin firaminista har sai lokacin da aka miƙa su a hukumance.

Hakan na zuwa ne sa’o’i kaɗan da dakarun adawar suka karɓe birane da dama a ƙasar.

Tuni ƴan adawar suka gabatar da jawabin farko a tashoshin labarai.

Wata majiya ta ce har an sako fursunonin Damascus dake tsare na tsawon lokaci a kurkuku.

Ƙasashen Ƙatar, Saudiyya, Jordan, Misira, Iraƙi, Iran, Turkiyya da Rasha sun fitar da wata sanarwar haɗaka inda suka ce yaƙin abu ne mai haɗari, su na masu kira da a samar da mafita ta siyasa.

A shekarar 2000 ne Bashar Al-Assad mai shekaru 59 ya ɗane karagar shugabancin ƙasar bayan rasuwar mahaifinsa, Hafez Al-Assad wanda ya jagoranci ƙasar tun daga 1971.

Ana zargin hamɓararren shugaban ne laifuka da dama da suka shafi karya dokar ƴancin ɗan-adam ciki har da amfani da makamai masu guba a yaƙe-yaƙen da ake yi a ƙasar.

By Babaji