HOTUNA: A wani yanayi na nuna kulawa ga ma’aikatan ofishinsa, Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya halarci ɗaurin auren ƴaƴan dogarinsa, Alhaji Ahmad Muhammad Idris, mata, wato Rahma da Zainab, waɗanda aka ɗaura a ranar Asabar, 7 ga Disamba, 2024, a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya