Babu sansani sojojin waje a Nijeriya – Janar Musa ya ƙaryata jita-jitar yarjejeniya da Faransa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya ƙaryata batun da ke cewa an bai wa Faransa damar kafa sansanin sojoji a Nijeriya.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara Faransa inda ƙasashen biyu suka cimma yarjejeniya game da ababen da suka haɗu a kai musamman kan harkokin tattali da makamantansu, ya na mai cewa babu wani layi acikin yarjejeniyar da ya bada damar samar da sansanonin sojojin waje a Nijeriya.

Janar Musa na magana ne a bikin buɗe bajin sojoji (Tattoo Logo) na shekarar 2025, a Hedikwatar Tsaro dake Abuja inda ya ce wannan maganar ba ta daga cikin abubuwan da aka amince da su.

Babban Hafsan ya faɗa da babbar murya cewa babu wata ƙasa da za ta kafa sansanin sojoji a Arewaci ko Kudanci ko ko’ina a faɗin Nijeriya.

Ya kuma jaddada muhimmancin cimma yarjejeniya da ƙasashen waje akan harkokin da suka shafi karɓar horo da haɗin kai a aikin sojoji, amma ban da bada dama ga wata ƙasa ta kafa sansanin soji.

By Babaji