
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta kashe Naira biliyan 21 wajen samar da da takin zamani ga manoman jihar a wannan shekarar.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kuɗin 2025 a zauren Majalisar Dokokin jihar a kwanakin baya.
Ya ce takin zamani ton 20,000 da aka sayar wa manoma 350,000, an samar ne a bisa farashi mai rahusa.
Bugu da ƙari, ya bayyana cewa gwamnati kuma ta tallafa wa manoman rani 2,040 da kayan aikin gona da kuɗinsu ya kai Naira 1.9bn.
“Kayan aiki noman sun haɗa da injinan ban ruwa da irin shuka daban-daban tare da magungunan feshi da sauran su” inji gwamnan.
Raɗɗa ya kuma ce a ƙoƙarin gwamnatinsa na bunƙasa harkar noma a jihar, ta sayi taraktoci 400 akan kuɗi Naira biliyan 12 domin tallafa wa manoma wajen yin noman zamani.
Haka kuma ya ce gwamnatinsa ta tallafa wa mata manoma 4,426 da suma suke amfani da kayayyakin aikin noma.
Har’ilayau gwamnan ya sanar da kashe kudi Naira biliyan 8 wajen sayowa da rarraba injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana guda 4,000 tare da wasu injinan ban ruwa da aka raba wa manoman rani akan farashi mai sauƙi.
Ya bayyana wa majalisar matakai da dama da gwamnatinsa ta ɗauka wajen bunƙasa harka noma.
Gwamnan ya shaidawa ƴan majilisar cewa waɗannan matakai da gwamnatin nasa ta ɗauka ya taimaka wajen samun amfanin gona mai yawa a jihar duk da barazanar ƴan bindiga a yankunan da aka fi yin noma.
“A shekara 2023, malaman aikin gona guda 78 ne a faɗin jihar amma ya zuwa yanzu da muka kafa gwamnati mun ƙara yawansu zuwa 772”, inji shi.
