‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan sanda a Katsina sun sami nasarar kuɓutar da mutane 20 daga hannun ‘yan ta’adda a lokacin da su kai ƙoƙarin sace mutanen a ƙananan hukumomin Jibiya da Faskari.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar ‘yan sanda a Jihar Katsina ASP Sadiq Abubakar Sadiq ya bayyana wa manema labarai haka a wata takarda ɗauke da sa hannun sa.
Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da ta wuce a Magaman Jibiya inda ƴan bindigan ɗauke da bindigar AK47 suka tare wata motar fasinja a ƙoƙarin su na karkatar da fasinjoji zuwa cikin daji.
Sai dai jami’an ƴan sanda na garin Jibiya suka kawo masu ɗauki,bayan ɗauki ba daɗi da ‘yan ta’addan, ‘yan sandan sun sami nasarar kuɓutar da fasinjoji guda 10 ba tare da ko kwarzane ba.
“Haka kuma a wannan rana cikin dare ƴan ta’addan suka shiga ƙauyen Bangori da ke kan hanyar Funtua zuwa Gusau nan ma suka tare motar fasinja ɗauke da mutum 10” Sadiq ya faɗi haka
Nan ma ‘yan sandan da ke kai wa da komowa a yankin suka sami labarin yan ta’addan,a nan ma bayan sunyi ɗauki ba daɗi da ƴan bindigan, yan sandan suka kuɓutar da fasinjojin dukan su guda 10 . ASP Sadiq ya ce.
“Sai da mutum ɗaya ya sami rauni shima yana nan a asibitin Faskari yana samun magani”ya bayyana haka.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar CP Aliyu Abubakar Musa ya jinjina wa jami’an tsaron da suka ceto waɗannan mutanen a Jibiya da Faskari bisa ƙwarewa da jarumtaka da suka nuna.
Ya kuma jaddada ƙudirin jami’an sa na cigaba da yaƙar ƴan ta’adda da sauran ɓata gari har sai zaman lafiya da walwala na jama’a ya dawo a jihar.
