Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa adadin ‘yan ta’addan Boko Haram 129,417 da iyalansu su ka miƙa wuya ga jami’an tsaro tsakanin 10 ga watan Yuli zuwa 9 ga Disamba, 2024.
CDS ya bayyana haka ne a taron tsaro na Afrika karo na 18 da ake gudanarwa a birnin Doha na ƙasar ƙatar wanda wakilin Daily Trust ya sanya wa ido manhajar zoom.
Taron ya samu halartar mahalarta daga Najeriya, Guinea Bissau, Gambia, Afirka ta Kudu, Kenya, da ƙatar.
Janar Musa a jawabinsa ya bayyana cewa alkaluman sun hada da mayaka 30,426, mata 36,774, da yara 62,265.
A cewarsa, wannan nasara ta nuna ci gaban da ake samu wajen samun zaman lafiya a tsakanin al’umma da ke bunƙasa zamantakewa da tattalin arziki a Nijeriya.
