An yaudari Gwamnan Kebbi da ma’aikata kan sabon albashi na N70,000 

Spread the love

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi 

Akwai yiwuwar ko dai ma’aikatan ƙananan hukumomi da malaman firamare a Jihar Kebbi su yi bore ko su tsunduma cikin yajin aiki ko kuma a sake lale dangane da maganar sabon albashi na Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, saboda tun watan goma da aka ƙaddamar da shirin sabon albashin ba a biya su ba, aka ce akwai waɗansu ‘yan gyare-gyare da za a yi da zummar za a biya bayan sati biyu, sai ga shi har watan ya ƙare ba a biya ba har kuma zuwa watan goma sha ɗaya, inda aka biya albashin, amma sai dai lokacin da aka biya albashin sai murna ta koma ciki saboda sun koka bisa ga yadda aka biya albashin a watan goma sha ɗaya.

Ma’aikatan ƙananan hukumomi da kuma malaman firamare a jihar sun koka bisa ga yadda aka biya albashin inda wani ma’aikaci mai matakin albashi na goma sha huɗu (Gl-14) kuma darakta da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa wakilinmu da cewa albashin sa bai wuce sittin da biyar ba ballantana na waɗanda ba su kai irin na sa matsayin ba.

Ya ƙara da cewa wannan maganar gaskiya ba a zartar da albashin kamar yadda aka yi sharaɗi ba saboda haka suna ganin ɗayan biyu ne, ko dai an yaudari gwamnan daya ofishin babban odita da kuma ma’aikatar ƙananan hukumomi da masarautu ko kuma shi gwamnan ne ya yaudari ma’aikatan saboda tun farko gwaman ya fito kafafen yaɗa labarai ya yi alƙawarin da zarar gwamnatin tarayya ta aiwatar da wannan albashin shi ma zai biya kowane ma’aikaci albashin mafi ƙaranci na dubu saba’in sai ga shi an yi amma kuma a jihar Kebbi an yi wani zurmuguɗɗu.

Wani ma’aikaci a hukumar ilmi da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyanawa wakilinmu da cewa su dai a nasu ɓangaren ba abinda za su ce saboda a Birnin Kebbi ne aka kitsa wannan badakalar ba a matakin ƙananan hukumomi ba kuma ba su ga laifin Gwama Nasir Idris ba saboda ya fito fili ƙarara ya shelantawa duniya da a biya kowane ma’aikaci albashin da ba zai kasa naira dubu saba’in a faɗin jihar in dai ba daga baya ne ya bayar da wani umarni na yi wa ma’aikatan ƙananan hukumomi da malaman firamare ƙafar Angulu ba.

Shugabannin hukumomin ilmin da wakilinmu ya nemi jin ta bakunan su da sauran manyan jami’an su ba su amince da su ce komai ba sai dai wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wannan ana hasashen ba ainihin karin albashin ba ne sai dai an yi gyara ne kan karin matakin albashi na kowane ma’aikaci da ke da karin matakin albashi amma ba kuma ba a biyan albashin wannan matakin amma maganar gaskiya ba a aiwatarda shirin mafi karancin albashi na dubu saba’in ba.

Ya kuma yi ƙarin haske dangane da cewa a matsayinsu na shugabanni sun nemi duk wani ma’aikaci da ke da ƙorafi ya rubuto ƙorafinsa tare da takardar biyan albashin daga bankunansu (bank payslip) don tabbatar da gaskiyar ƙorafe-ƙorafen su inda su kuma za su ɗauki ƙorafin zuwa shalkwata.

Haka-zalika a ƙananan hukumomi ashirin da ɗaya da ke akwai faɗin jihar duk maganar ɗaya ce don kuwa har yanzu wannan lokacin da aka ce an yi wannan gyaran albashin mafi yawancin ma’aikatan suna karɓar naira dubu goma sha biyar ne zuwa arba’in.

Jam’iyyar PDP ta adawa a jihar Kebbi ta dirarwa ƙungiyar ƙwadago ta reshen inda a wata takarda mai ɗauke da sa hannun Alhaji Sani Dododo Kakaakin yaɗa labarai da aka raba wa manema labarai ranar Litinin 9/12/2024 ta bayyana rashin gamsuwarta bisa ga yadda ƙungiyar ƙwadagon ta koma ‘yar amshin shatan gwamnati da ake hada baki da ita ana tatsar mai daga jikin ma’aikatan a maimakon ta tsaya tsayin daka din ganin ta nemowa ma’aikatan gwamanti, kamfanoni da dai sauransu haƙƙoƙansu kamar yadda ya ke a tsarin ƙwadago.

Binciken da wakilinmu ya yi dangane da wannan badaƙalar ta albashin ƙananan hukumomi da malaman firamare a jihar Kebbi ya nuna duk da ya ke dai akwai hasashen akwai alamun mugu-mugu a ciki akwai waɗansu da wannan ƙarin ya amfana a cewar wani Muhammed Yusuf,” Ni gaskiya wannan karin albashin na ji dadin sa saboda yau Ina da kusan shekaru ashirin Ina aiki a hukumar ilmi amma ba a taba kara min albashi ba saboda Ina karbar dubu gonna Sha bakwai amma yanzu albashi na ya kai kusan hamsin da biyar,” inji shi.

Sai dai wani abin mamaki da kuma ya ɗaurewa al’ummar jihar ta Kebbi musamman malamai kan gwamna Malam Nasir Idris, lokacin da aka zaɓe shi a matsayin gwamna malamai musamman na firamare sun shiga murna saboda bayan kasancewarsa tsohon malamin firamare Shugaba ne na ƙungiyar malamai ta kasa saboda haka suna kyautata masa zaton lokacin nemowa tare da biyan hakkokansu ya zo sai ga shi abin ya zo akasin haka duk da ya ke mafi yawancin malaman firamare musamman wadanda suka kusance shi sun nuna cewa yaudarar sa ne aka yi saboda wadansu jami’an gwamnati ne da ya baiwa amana suka  azurta kawunansu shi kuma su shafa masa kashin kaji bisa ga kudurinsa na sake tsayawa rakara a karo na biyu a shekarar 2027 idan Allah ya kai mu saboda albashin farko da ya kamata a biya kowa a maimakon haka ba a biya ma’aikatan Ƙananan hukumomi da Malaman firamare ba da zummar za a biya amma dai ga dukkan alamu an yi watanda da kudaden albashin su na watan goma sai dai lahira idan gwamnan bai tilasta wa babban odita da makarabbansa biyan albashin ba.

By ukarofi