Muna horar da matasa da ɗaukar su aiki – Sani Diso

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano 

Shugaban kamfanin samar kujerun zamani da dangoginsu da ke Kano, Alhaji Sani Diso, wanda aka fi sani da Uncule, ya bayyana cewa wannan kamfani na iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya ba al’ummar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya gudunmawa ta fuska ɗaukar matasa aiki da kuma horar da su ta hanyar ɗorasu akan kyakkyawan tsari da tarbiyya yadda za a samu bunƙasar tattalin arziƙi da tsaro.

Sani Diso ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da wakilinmu ya yi da shi cikin satin nan a Kano.

A ƙarshe Sani Ancule, ya ƙara da cewa matasa ɗalibai kan zo daga makarantu fasaha su samu horu a aikace a wannan kamfani duk shekara, kan wannan ne ya nemi gwamnatin Kano bisa jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf da sauran masu ruwa da tsaki da agaza musu kamar yadda a Kano gwamnati take taimakawa ilmi da sauran fannonin rayuwar al’ummar Kano da kuma ɗaukar matakai wajen kawo ƙarshen matsalolin hasken wutar da ke kawo cikas musaman a Kano, Arewa da ma Nijiriya baki ɗaya.

By ukarofi