Mai aikin shara ya mayar da miliyan N40 da ya tsinta a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani mai aikin sharar asibiti a Kano ya mayar da kuɗin da ya tsinta kimanin Naira miliya 40 ga mai su.

Malam Aminu Umar Kokar Mazugal ya tsinci kuɗin ne a dalolin Amurka a cikin wata jaka da mai su ya manta a Asibitin Abubakar Imam da ke Unguwar Fagge.

Malam Aminu wanda matsakaicin ma’aikaci ne ya tsinci kuɗin a cikin wata jaka kuma ya mayar da kuɗin ga mai su, Alhaji Ahmed Abubakar, wanda ya manta da su a lokacin da ya je dubiyar mara lafiya a asibitin.

Alhaji Ahmed ya manta da kuɗin ne a wurin da ya ɗan zauna na ɗan lokaci a wurin ajiye motoci da ke kusa da masallaci, inda daga bisani ya wuce domin shiga jirgin sama.

Malam Aminu ya shaida wa wakilinmu cewa jim kaɗan da tafiyarsa mutumin ne shi kuma ya tsinci kuɗin a lokacin da yake aikin shara.

Ya ce daga bisani, bayan kimanin awa guda, mai kuɗin ya dawo yana cikiya, shi kuma ya mayar masa kayansa.

Ya ce mai kuɗin ya yi masa kyauta amma ya ƙi amsa, duk da cewa ya ba shi lambar wayarsa, kuma mutumin ya yi alƙawarin tuntuɓar sa idan ya dawo daga ƙasar waje.

Shugaban Asibitin, Dokta Aminu Imam Yola, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa hukumar gudanarwar asibitin ta sanar da Ma’aikatar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano domin a karrama Malam Aminu.

By ukarofi