Dubban ‘yan PDP, APGA, YPP sun sauya sheƙa zuwa APC a Jihar Zamfara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Ya’yan Jam’iyyar PDP su 1,500 da APGA da YPP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a jihar Zamfara.

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Jamilu Iliyasu, mai taimaka wa shugaban kwamitin asusun kula da yanayin ƙasa kuma mai wakiltar Birnin Magaji/Kaura Namoda a majalisar wakilai, Jaji, ya fitar a ranar Litinin na Gusau.

Ya ce waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da shugabanni da magoya bayan jam’iyyar PDP da APGA da YPP da wasu jam’iyyu a jihar.

Shugaban ƙungiyar jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Isiyaka Ajiya-Anka, wanda ya wakilci ɗan majalisar, ya yaba da matakin da masu sauyin sheƙar suka ɗauka tare da bayyana hakan a matsayin cigaba ga jam’iyyar APC.

Jaji ya ba wa sabbin ‘yan jam’iyyar tabbacin cewa yanzu an zama ɗaya kuma za a haɗu ne a yi aiki tare wajen cigaban jam’iyyar inda ya ce darajar shugabannin da suka dawo jam’iyyar abu ne da zai ƙara ɗaga martabar tafiyar tasu.

A cewar Iliyasu, jigajigan ‘yan jam’iyyar da suka dawo APC sun haɗa da tsohon jam’iyyar APGA, Alhaji Rabi’u Salisu-Bature, tare da ɗaruruwan magoya bayansa.

Sauran kuma akwai shugaban jam’iyyar YPP, Alhaji Sani Anka, tare da magoya bayansa.

Har’ila yau akwai shugaban ‘yan siyasa daga ƙaramar hukumar Shinkafi da tsohon darakta-janar, Alhaji Nasiru Yusuf da shugaban jam’iyyar PDP a Shinkafi Malam Ibrahim Tado.

Haka kuma akwai shugabar mata ta jam’iyyar PDP a ƙaramar hukumar Shinkafi, Hajiya Abu Alasan, da shugaban matasa na PDP, Lukman Hamidu.

Sannan Iliyasu ya ce, saura waɗanda suka sauya sheƙar akwai Hajiya Zainab Aliyu wacce lauya ce da Mas’udu Wada da Babangida Adamu da sauran magoya bayan jam’iyyar.

By ukarofi