Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Korar Samuel Aruwan, tsohon kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna daga majalisar ministocin Gwamna Uba Sani ya ƙara ta’azzara cece-ku-ce game da tsamin dangantaka tsakanin gwamnan mai ci da kuma wanda ya sauka, Nasir El-Rufai.
Fitar Aruwan dai ba ta kasance ba kwata-kwata, domin rahotanni sun nuna cewa ana takun saƙa tsakanin mambobin gwamnatin da ke da alaƙa da tsohon gwamnan.
Aruwan, wanda tsohon ɗan jarida ne, ya taɓa zama mai bai wa El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a daga shekarar 2015 zuwa 2019. Bayan zaɓen 2019, an naɗa shi kwamishina na farko a sabuwar ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida da aka kafa, matsayin da ya ƙara masa ɗaukaka da tasiri matuƙa a gwamnatin El-Rufai.
Majiyoyin da ke kusa da gwamnatin sun bayyana cewa Aruwan ya samu ‘yancin cin gashin kansa sosai saboda alaƙarsa da El-Rufai, kuma ya taka rawa wajen goyon bayan takarar Gwamna Uba Sani, duk da cewa tun da farko El-Rufai ya na da ra’ayin tsayawa takarar Sani.
Duk da gudunmawar da ya bayar, Aruwan ba a sake naɗa shi kwamishinan tsaro na cikin gida ba bayan da Sani ya hau kujerar. Maimakon haka, ya yi hidima a matsayin mai kula da ma’aikatar fiye da shekara guda yayin da aka tabbatar da wasu kwamishinoni. Bugu da ƙari, an naɗa shi shugaban hukumar babban birnin Kaduna, muƙamin da ya riƙe tare da aikinsa a ma’aikatar tsaron cikin gida.
Yayin da gwamnatin da ta gabata ciki har da Aruwan ke fuskantar zargin karkatar da naira biliyan 423 da majalisar dokokin jihar ta yi, ya ci gaba da zama a cikin majalisar Sani. Sai dai rahotanni sun ce wasu daga cikin abokan Sani na kallon ci gaba da kasancewarsa a matsayin wata matsala, inda suka yi kira da a cire mutanen da ake ganin suna biyayya ga El-Rufai.
Daga ƙarshe dai an tsige Aruwan tare da Shizzer Bada tsohon kwamishinan kuɗi da Tijjani Abdullahi shugaban zartarwa na hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar. Korar nasu ya biyo bayan wata takarda da hukumar Code of Conduct Bureau (CCB) ta yi, wadda ta yi zargin cewa sun bayyana kadarorin su na ƙarya.
Korar waɗannan jami’ai da ake yi wa laƙabi da masu biyayya ga El-Rufa’i, ya ƙara zafafa zargin siyasa. Gwamnatin jihar Kaduna dai ba ta bayar da wani bayani a hukumance kan korar su ba, lamarin da ya ƙara janyo cece-kuce a tsakanin Sani da El-Rufai.
Wani tsohon kwamishina a ƙarƙashin El-Rufai, da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa korar da aka yi ta siyasa ce kawai.
“Abin da ya faru da Aruwan da sauran su na da nasaba da siyasa. Gwamnati mai ci ba za ta iya keɓe kanta daga hakan ba,” inji majiyar.
Tsohon kwamishinan ya ƙara da cewa, “Ga Samuel Aruwan, maganar gaskiya yana cikin wannan hali ne saboda mai biyayya ne ga tsohon gwamnan. Ba shi kaɗai ba, har ma wasu tsofaffin kwamishinoni a ƙarƙashin El-Rufa’i na fuskantar bincike daga EFCC, ICPC da Code of Conduct Bureau.”
Majiyar ta kuma alaƙanta soke wasu manyan hukumomi uku da gwamnatin El-Rufai ta haifar da rikicin da ake zargin cewa shugabannin waɗannan hukumomin duk El-Rufai ne ya naɗa.
Hakazalika, wani tsohon shugaban jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) a jihar ya bayyana cewa korar da aka yi an mayar da ita ne a matsayin wani yunƙuri na gudanar da bincike amma a zahiri wani mataki ne na kawar da masu biyayya ga El-Rufai daga gwamnati.
ƙoƙarin jin ta bakin Malam Ibraheem Musa babban sakataren yaɗa labarai na gwamna Uba Sani ya ci tura, domin bai amsa kiran waya da saƙon kartakwana ba.
Sai dai wata majiya a cikin gwamnatin da ta gwammace a sakaya sunanta, ta yi watsi da zargin da ake yi na ɓaraka da cewa ba shi da tushe balle makama.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Korar Samuel Aruwan da Shizzer Bada, kwamishinonin tsaro na cikin gida da kuɗi, ba shi da alaƙa da abin da ake kira ɓaraka da ke wanzuwa sai tunanin ma’aikatan siyasa da kafafen yaɗa labarai.
A cewar majiyar, korar ta biyo bayan umarnin kotu da ta bayar a watan Oktoba bayan wani ƙorafi da aka shigar a gaban kotun ɗa’ar ma’aikata.
Gwamnati ta gargaɗi waɗanda aka naɗa kan rubuce-rubucen da ba su dace ba a shafukan sada zumunta.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta gargaɗi masu riƙe da muƙaman siyasa a kan abin da ta kira yaɗa labaran da ba su dace ba, tana mai gargaɗin cewa irin waɗannan ayyuka na iya cutar da martabar gwamnatin.
An bayar da wannan nasihar ne a cikin sanarwar bayan wani taron ƙarawa juna sani na kwana biyu da ofishin shugaban ma’aikata da babban sakataren gwamna Uba Sani suka shirya.
Taron wanda aka gudanar daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Disamba, ya jaddada buƙatar ɗa’a, biyayya da ƙwarewa a tsakanin ma’aikatan gwamnati.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Alhaji Waziri Garba babban mataimaki na musamman kan harkokin mulki da kuma Malam Ibraheem Musa, babban sakataren yada labarai, ya bayyana cewa za a iya yin amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo da bai dace ba da waɗanda aka naɗa ke yi a matsayin matakin gwamnati, wanda hakan zai janyo cece-kuce a tsakanin jama’a ko kuma ɓata suna.
