Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai.
A dukkan sha’ani na mulki, da kuma tsarin shugabanci na mulkin soja ko farar hula mai taken (Dimokraɗiyya), babban al’amarin da ya dace ayi don ci gaban al’umma da ƙasa ko jiha bai wuce samar da zaman lafiya ba.
Ko shakka babu, zaman lafiya a tsakanin al’umma, shi ne babban tushen haɓakar arziki da ciyar da ƙasa ko yanki gaba, kuma shi ne ginshiƙin raya ƙasa da al’ummar ƙasa. Wannan shi ne batu na gaskiya, kuma shi ne abinda ya dace a ce an maida hankali a kai don ganin cewa Nijeriya ta kakkaɓe talauci da fatara gami da kawo ƙarshen cin hanci da rashawa a tsakanin mutane.
A makonni biyu da suka gabata, an ga yadda maigirma gwamnan jihar Kaduna ya tashi ƙafa-da-ƙafa zuwa ƙaramar hukumar Birnin Gwari don zaman sulhu tsakanin ‘yan bindigar da ke ayyukan fashi da garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa, wanda aka gudanar da shi a ƙaramar hukumar, ranar Alhamis 30 ga watan Nuwambar 2024 da ya gabata, inda aka yi zaman don kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci, tare da ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da juna, kuma hakan ta tabbata har hankula sun kwanta a yanzu, kuma kowa yana hulɗarsa cikin daɗin rai.
Ko shakka babu wannan babban abin alfahari da farin ciki ne, kuma abin a yaba ne tare da jinjina ga mai girma Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani, domin kowa yana sane da irin abubuwan da suke faruwa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, na rashin tsaro da ya haifar da asarar rayuka da ɗimbin dukiya, baya ga tashin al’umma da garuruwansu da masu ayyukan ta’addanci suka yi a yankin.
ƙaramar hukumar Birnin Gwari, Allah ya albarkace su da ƙasar noma mai tarin albarka, ga ma’adanai da sauran su. To amma kuma sai ya kasance yankin ya durƙushe a sakamakon ayyukan ‘yan bindiga. Duk da cewa jami’an tsaro suna iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an kawi ƙarshen ayyukan ‘yan bindiga a yankin, amma sai al’amarin yayi ƙamarin da kullum ake rasa ina matsalar take.
Sakamon ayyukan fashi, sata da garkuwa da mutane da ake yi a yankin, hakan ya tilastawa mazauna yankin kasa yin noma a lokacin damina, noman da ake samar da kayan abinci nau’i-nau’i, da dangin kayan marmari da dama. A iya ƙaramar hukumar Birnin Gwari kaɗai, ana iya samar da tan miliyan ɗaya 1m na abinci a lokacin kaka. To amma a sakamakon ayyukan ‘yan bindiga sai noman ya koma kaso 10 cikin ɗari, ya zamana ga gonakin nomawar amma ba za su nomu ba saboda barazanar tsaro.
Yanzu da Maigirma Gwamna Malam Uba Sani yayi abinda yayi na ƙoƙari aka samu zaman lafiya, ko shakka babu wannan namijin ƙoƙari ne, ƙoƙari irin na yunƙurin sauke nauyin al’umma a cikin shugabanci nagari, wanda kuma hakan abin a yaba ne ga maigirma Gwamnan jihar Kaduna. Domin kamar yadda ya faɗa a cikin jawabansa cewa, “Gwamnati ba za ta iya samar da makarantun ilimi, hanyoyin sufuri, wutar lantarki, ruwan sha, asibitoci da makamantansu ga al’umma ba sai da zaman lafiya…” Tabbas wannan haka yake, idan akwai zaman lafiya ne kaɗai gwamnati zata iya samar da abubuwan ci gaba ga mutane, wanda kuma hakan ba zai yiwu ga gwamnati kaɗai ba har sai suma mutane sun bada haɗin kai.
Mai girma gwamna muna jinjina maka, kuma muna yaba wa da abinda aka yi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, na daidaita tsakanin al’ummar gari da mutanen daji da suke ayyukan ta’addanci, aka jawo hankulansu tare da nuna musu illa da rashin dacewar abinda suke aikatawa, har kuma suka yarda suna aikata ba daidai ba kuma suka ajiye makamai suka bari.
Tabbas ni na gani da idona ba labari a ka bani ba, a yanzu haka tunda aka yi wannan zama ƙarƙashin jagorancinka maigirma Gwamna, zaman lafiya ya samu a ƙaramar hukumar Birnin Gwari. An daina tare hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna a kwashe mutane matafiya a mota, ko a buɗe musu wuta, ko a shiga ƙauyuka ayi sata da ƙwace ko a kashe jama’a. Haka nan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtuwa an dawo yin amfani da ita bayan shekaru sama da goma da ta kasa biyuwa.
Tunda aka yi wannan zaman sulhu al’ummar Birnin Gwari da kewaye suka samu kwanciyar hankali, aka samu ƙarin yalwar arziki, kasuwancin da aka rasa a tsawon shekara sama da goma, yau ya dawo tamkar a baya. Mutanen ƙauye da suke kasa sayen abin amfani don jin daɗin rayuwarsu da cin moriyar noman da suka yi, yau sun samu sukunin sayen sabbin baburan hawa da motocin hawa da na haya, wanda a da basu isa su saya ba koda suna da kuɗin, ba don komai ba sai don tsoron kada su saya a mutanen daji su ƙwace, ko a kama mutu ace yana da kuɗi ayi garkuwa dashi a nemi kuɗin fansa.
A cikin sati biyun nan kaɗai da yin wannan sulhu, mutanen yankin Birnin Gwari sun samu nutsuwar da ta gushe a gare su da kaso 90 a cikin ɗari, sakamakon kaso 10 cikin 100 a baya ta nutsuwar da suke da ita. Wannan abu da Maigirma Gwamna Malam Uba Sani yayi, abin ayi koyi dashi ne a sauran jihohinmu na Arewa da ake fama da ayyukan ‘yan bindiga, irin su; Niger, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Katsina.
Yin sulhu da ‘yan ta’adda a wannan yanayin da muke ciki a Arewacin Nijeriya da Gwamnatocin yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro ba gazawa ba ce, ana kallon maslahar al’umma ne. Domin al’amari ne da ya zama ana yin tufka ta baya na warwara ne, ana ƙoƙarin kawo ƙarshen lamarin da ƙarfin bakin bindiga, amma kuma wasu marasa kishin ƙasa suna ƙara iza wutar rikici. Akwai irin waɗannan mutane a cikin al’ummar gari, da jami’an tsaro, da kuma wasu a cikin manyan ƙasa masu riƙe da sarautar gargajiya da manya a cikin gwamnati, da kuma talakawa da zuciyarsu take ribatarsu a kan kwaɗayin abin duniya.
Sannan a wannan gaɓar, ina baiwa maigirma Gwamna shawara a kan, lallai ya kamata a riƙa bibiyar wannan sulhun zaman lafiya da aka samar tsakanin al’ummar gari da ‘yan bindiga don daƙile duk wasu da za suyi yunƙurin wargaza wannan zaman lafiya da aka samu. A sa ido sosai, a ci gaba da wayar da kawunan waɗancan mutane da suka yarda suka ajiye makamansu don su zamo mutanen ƙwarai, kada su koma cikin wancan aiki da suke yi a baya.
Nayi imani cewa, tilas sai an samu waɗanda za su ji babu daɗi a kan wannan zaman lafiya da aka samu, domin suna yin amfani da wannan suna samun kuɗaɗe, duk da cewa ta haramtacciyar hanya suke samun kuɗin, amma su ba za su kalli abin a matsayin gurɓataccen al’amari mai muni ba, ba za su kalli kansu a matsayin maciya amanar ƙasa da al’ummar ƙasa ba, face za su kalli cewa sun rasa hanyar samun kuɗaɗe ne kawai.
Ya mai girma Gwamna, ayi duk mai yiwuwa don tabbatar da zaman lafiya ya ɗore ba a iya ƙaramar hukumar Birnin Gwari kaɗai ba, har da dukkan sauran ƙananan hukumomi da unguwanni a ciki da wajen gari. Hakan shi zai samar da ƙaruwar arziki a Jihar Kaduna, tare da samar da nutsuwar yin rayuwa cikin aminci da tabbatar da ƙaunar juna don zamowa al’umma ɗaya.
A kwai unguwannin da suke fama da matsaloli na rashin zaman lafiya, yawan faɗace-faɗace a tsakanin matasa tare da shan miyagun ƙwayoyi, sace-sace da aikata miyagun laifuka, wanda hakan na taka rawa sosai wajen taɓarɓarewar tsaro da jawo matsala a zaman lafiya da gushewar nutsuwa a zukatan al’umma. Irin waɗannan unguwanni yana da kyau a ƙara sa ido a kansu, a kuma ci gaba da ɗaukar matakai da za su daƙile aikata miyagun laifuka a tsakanin al’umma (musamman matasa).
Don haka, ina kira ga Maigirma Gwamna a riƙa duba ƙoƙarin irin waɗannan bayin Allah su Major Shehu da suke bada gudummawa a cikin unguwanninsu don ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa. Hakan zai ragewa Gwamnati aiki, tare da samar da ƙaruwar arziki da kwanciyar hankali da samun matasa nagari ‘yan kishin ƙasa, ba ma su ƙoƙarin wargaza ci gaban ƙasa ko yanki ba.
Abin farin ciki da alfahari ne ga kowacce gwamnati ta samu jajirtattun mutane a kowacce unguwa da suke ƙoƙarin haɗa kan al’umma wajen zaman lafiya, hakan na ragewa gwamnati kashe kuɗaɗe wajen yaƙi da ɓatagari, da kuma samun sauƙin matsalar rashin tsaro da zaman lafiya. Da haka ne gwamnati take samun damar gudanar da mulki cikin salama, rashin irinsu kuma yana gurgunta tafiyar gwamnati a kowacce ƙasa da yanki, a riƙa ɗiban kuɗi maƙudai ana kashewa don samar da zaman lafiya amma hakan ta gagara.
A ƙarshe ina ƙara kira ga mai girma gwamna Malam Uba Sani, a kula da mutanen Karkara sosai. Tabbas mutanen karkara sun jijjiga, sun raunana kuma sun wahaltu matuƙa. Garuruwan da ‘yan bindiga suka tasa ayi duk mai yiwuwa wajen ganin sun koma garuruwansu, a kuma gina musu makarantu da asibitoci da samar musu da wutar lantarki, tare da gyara musu hanyoyin sufuri. Hakan zai sa mutanen da ke cikin birni su ragu, domin akwai ‘yan gudun hijira da yawa a cikin birni. Idan mazauna ƙauyuka suka koma garinsu, to noma zai ƙaru, abinci zai ƙara wadata sosai.
Ina yi wa maigirma Gwamna Malam Uba Sani fatan alkhairi, tare da addu’ar Allah Ya yi riƙo da hannayenka, Ya baka ikon sauke nauyin al’umma. Allah Ya ƙara kawo mana zaman lafiya a jihar Kaduna da Nijeriya baki ɗaya.
Daga NAFI’U SALISU.
Marubuci/manazarci. Daga Kano Nigeria. [email protected]@gmail.com.08038981211-09056507471.
