Gwamnatin Tarayya za ta samar da bankin matasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa bankin matasa don bayar da lamuni, tallafi da sauran kayayyakin kuɗi don tallafa wa matasa masu sana’o’in dogaro da kai wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da samar da ayyukan yi.

Ministan ci gaban matasa Mista Ayodele Olawande ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Talata a Abuja.

A cewar ministan, ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an samar da tsarin samar da ayyukan yi ga matasan Nijeriya domin magance matsalar rashin aikin yi a ƙasar.

“Kafa bankin matasa yana da fa’ida da dama ga matasa da al’umma.

“Ta hanyar tallafawa kasuwancin da matasa ke jagoranta, bankunan matasa na iya ba da gudummawa ga samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arziki.”

Ya ce bankin zai samar da damammaki na ilimi da horo da kuma samar da ayyukan yi.

Olawande ya ce ma’aikatar ta kuma ƙaddamar da jadawalin ayyukan matasa inda za a bajekolin ayyuka da tsare-tsare.

“Muna cewa kowa ya shiga wannan jadawali don samun bayanai.

“Mun gano cewa akwai ayyuka sama da 7,000 na matasa a Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomi (MDAs) da sauransu,” inji shi.

Ministan ya ce shirin bayar da lamuni na ɗalibai wani makami ne na yaƙi da talauci, inda ya ƙara da cewa shirin rancen ya yi daidai da ƙudurin gwamnatinsa na haɗa kai.

Ya bada tabbacin samun isassun kuɗaɗe don ɗorewar shirin.

Olawande ya ce ilimi shi ne babban makamin yaƙi da talauci a kowace al’umma domin yana da matuƙar muhimmanci ga hangen nesa, ci gaba da samun nasarar yaƙi da rashin tsaro da suka haɗa da ta’addanci da ‘yan fashin daji.

Ya ba da shawarar samar da yanayi mai ba da dama ga matasa su ci gaba da cimma burinsu na rayuwa.

A cewarsa, ƙasar na da sama da kashi 60 cikin 100 na matasa; don haka, ana iya samun da yawa tare da yanayin da ya dace.

Olawande ya ce ma’aikatar tana yanke shawara da shawarwari masu muhimmanci ga shugaban ƙasa Bola Tinubu domin aiwatarwa.

By ukarofi