Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Jigawa, ta gano ma’aikatan bogi 6,348, yayin tantance ma’aikatan jihar, wanda hakan ya taimaka wajen hana zurarewar kuɗi sama da Naira miliyan 314 a wata da kuma Naira biliyan 3.7 a shekara.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Dutse.
Ya ce an gano ma’aikatan bogi bayan tantancewa da gwamnatin ta gudanar ta hanyar ɗaukar yatsunsu, wanda aka shirya domin tsaftace tsarin biyan albashi a jihar.
“A yayin gudanar da wannan bincike, an gano ma’aikata 6,348 na bogi, wanda hakan ya rage wa gwamnati asarar Naira 314,657,342 a wata da kuma kusan Naira biliyan 3.7 a shekara,” inji Musa.
Ya bayyana cewa Majalisar Zartaswa ta Jihar, ta amince a kafa Cibiyar Tantance Ma’aikatan Jihar (CCC) a ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar.
“Wannan cibiya za ta taimaka wajen tantance tare da tallafawa tsarin domin tabbatar da ingantattun bayanan ma’aikata a nan gaba,” inji shi.
Musa, ya kuma jaddada cewa wannan bincike na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a fannin ma’aikata.
Ya ce matakan da nufin hana sake samun matsalolin biyan albashin ma’aikata na bogi a nan gaba.
Kwamishinan ya buƙaci ma’aikata da su bayar da haɗin kai yayin ci gaba da aikin tantancewar.
Har ila yau, ya ce tsarin zai taimaka wajen mayar da kuɗaɗe zuwa muhimman ɓangarori kamar ilimi, lafiya da gina ababen more rayuwa.
