Daga AISHA ASAS
Kamar yadda ake cewa, mutanen da su ne suka san yadda ake nema, don haka su suka san darajar kaɗan da ake biyan su. Idan muka kalli yadda ababe suka sawwaka, da yadda hanyoyin samu suka yawaita, za mu gane cewa, mutanen da albarka suka fi mu ba yawa ba.
Da wannan ne tsohon jarumi da har yau ake tafiyar da shi Chiwetalu Agu, ya janyo hankalin matasan jarumai don su san irin sa’ar da suka yi a harkar fim, ma’ana ko kusa ba sa shan wahala kamar yadda suka sha a harkar ta fim, kuma abinda matasan jarumai ke samu a harkar na baya ko ƙamshinsu ma ba su ji ba. Albarkacin gata da zamani ya yi masu ta hanyar samar masu hanyoyin amfani da baiwarsu su samu kuɗi ba tare da dogaro da wani na yinmasu hakan ba, wato masu shirya finafinai.
“Matasan jarumai na wannan zamanin ba za su gane irin sa’ar da suka yi ba a harkar fim ba, domin baiwarsu na samun karɓuwa daga ko’ina, kuma ba su da shinge ga bajekolin fasahar su, kasancewar an buɗe masu hanyoyi da yawa na samun damar amfana da irin baiwar da aka ba su, ba a bar su da dogaro da wasu tsirarun mutane da za su yi wa baiwarsu hisabi ba.
A namu lokacin, kokaɗan ba haka abin yake ba, ko kaɗan ba mu mora yadda suke mora yanzu ba. Za su dinga giɗaɗamu, da kiranmu da sunaye na manyan muƙamai da girmamawa, amma bayan mun gama wahalar, su ɗauko dubu goma ko goma sha biyar su ba mu a matsayin kuɗin aiki. Wani lokacin ma a bashi za a yi masu aikin wanda ba kasafai suka cika biya ba. Saidai kawai mu haƙura bayan mun gaji da bi.
Shahara dai kam an same ta ƙwarai, amma dai nauyin kuɗin cikin asusun ajiya na bankinmu ko daɗan ba ya tafiya tare da shaharar.”
Jarumi Chiwetalu Agu, ya kuma bayyana yadda kafafen sada zumunta suka zama wata hanyar cigaba ga jarumai a wannan zamani, dalilin samar da biya ga ayyuka irin waɗanda su jarumai ke yi ta hanyar yaɗawa.
“Lokacin da ɗana ya nuna min adadin kuɗin da akawon ɗina na kafar Facebook ke samarwa, na yi matuƙar jin daɗi, saboda a baya can sai na yi aiki mai yawa, da amfani da manya-manyan kalmomin Turanci a fim kafin in iya samun kuɗin da suka kai dubu goma sha biyar.”
