
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su kasance masu kyautata zato da tsammanin cimma nasarori yayin da ake gudanar da bukukuwan ƙarshen shekara.
A cikin wani saƙo na musamman ga al’umma da ke ɗauke da sanya hannunsa, Shugaba Tinubu ya taya mabiya addinin Kirista murnar Kirsimeti da fatan alheri a sabuwar shekara ta 2025 dake cigaba da ƙaratowa.
Ya ce Kirsimeti lokacin ne na nuna godiya ga Ubangiji da kuma yaɗa soyayya, zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.
Yace duk da cewa ƙasar tana fama da matsaloli a sassanta, ya yi imani cewa Ubangiji yana tare da al’ummar, ya na mai bada misali da iftila’in da suka faru a Ibadan da Abuja da Okija na jihar Anambara inda mutane da dama suka rasa rayukansu tare da wasu da suka jikkata.
Tinubu ya jajenta wa mutane da iyalan waɗanda iftila’in ya shafa da waɗanda ambaliya, gobara ko ma haɗurra suka shafe su a wurare mabanbanta inda kuma ya yi musu addu’ar samun tsari daga faruwar irin haka a nan gaba.
Haka kuma ya yi fatan samun tsari ga matafiya yayin da suka tafi garuruwansu da kuma lokacin dawowarsu.
