Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya ƙaddamar da rabon injinan noma na hannu guda 4,000, famfunan ruwa masu amfani da hasken rana guda 4,000, da buhunan takin zamani guda 48,000 ga manoma a faɗin jihar.
Taron ya gudana a ranar 23 ga Disamba, 2024, a Dandalin Jama’a na Fadar Gwamnati, Muhammadu Buhari House, Katsina.
A jawabinsa na maraba, Kwamishinan Ma’aikatar Noma ta Jihar Katsina, Farfesa Ahmad Mohammed Bakori, ya jero wasu daga cikin ayyukan bunƙasa noma da gwamnatin Radda ta aiwatar don inganta aikin gona. Ya kuma jinjina wa Gwamna Dikko Raɗɗa a madadin manoman Jihar Katsina, saboda goyon bayan da suke samu.
Ministan Noma da Tsaro Abinci na Tarayya, Injiniya Abu Kyari, wanda ya halarci taron, ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Raɗɗa wajen inganta harkar noma a Jihar Katsina. Ya kuma bayyana irin gudummawar da ma’aikatarsa ta bayar ga jihar a fannin noma.
A jawabinsa, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya gode wa Shugaban Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bisa tallafin da ya bai wa jihar ta hanyar samar da kayayyakin aikin gona daga Ma’aikatar Noma ta Tarayya. Ya kuma gode wa Minista bisa halartar taron duk da cunkoson jadawalinsa.
Gwamnan ya lissafa muhimman ayyukan noma da gwamnatinsa ta aiwatar daga Janairu zuwa Disamba 2024. Ya kuma bayyana cewa zaɓin waɗanda suka ci gajiyar tallafin an yi shi ne ta hanyar kwamitocin shugabannin al’umma (CLC) bisa cancanta.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga ma’aikatan tallafin noma da shugabannin al’umma su sanya ido kan yadda za a yi amfani da kayayyakin da aka raba don ganin an yi amfani da su yadda ya dace.
