DAGA MUKHTAR YAKUBU
An ɗauki tsawon lokacin da masu kallon finafinan Hausa musamman na Kannywood suke kan yadda finafinan suka tsaya iya bayar da labarin soyayya da nuna ta’addanci, domin kusan duk wani fim da za su kalla sai su ga jigon labarin soyayya ne da ‘yammata da samari, ko kwartanci ko kuma nuna harkar daba, hakan ya sa ake ganin kamar masu shirya fim sun mayar da soyayya da cin amana da ta’addanci kamar wasu muhimman abubuwa a cikin Al’adun ƙasar Hausa.
Sai dai a yanzu za a iya cewa an fara samun sauyi da kuma canzawar tunani ga masu gudanar da harkar fim ɗin wadda ake ganin hakan zai iya kawo wani gagarumin sauyi a cikin harkar finafinan Kannywood.
Domin kuwa a daidai wannan lokacin fitaccen furodusa Naziru Alkanawy ya yi wani yunƙuri na fitar da wani sabon fim mai suna ”Muhalli” wanda ya zo da wani sabon salon labari a cikin finafinan da aka saba gudanar da su a cikin Kannywood.
Fim ɗin ”Muhalli” wanda a yanzu ake kan aikin sa a cikin garin Kano ya samu tsaruwa tun daga labarin har zuwa lokacin gudanar da aikin ta fuskar nuna ƙwarewa da basira a tsarin rubutun labarin da kuma tsara shi wanda shi Naziru Alkanawy da kansa ya tsara kuma ya rubuta labarin a matsayin sa na ƙwararre a fannin rubutun labarin fim da tsara shi tsawon lokaci.
Haka nan an samu mai bada umarni wato darakta tsohon hannu a cikin harkar, wato Ali Rabi’u Ali Daddy wanda ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka shafe tsawon lokaci ana damawa da su a cikin harkar fim don haka ne muka ji ta bakin sa a game da yadda aikin fim ɗin yake gudana a matsayin sa na mai bada umarni, inda Ali Rabi’u Ali Daddy ya fara da cewa.
“To shi dai wannan fim ɗin da muke gudanar da aikin sa a yanzu sunan sa ‘Muhalli’, kuma yana daya daga cikin tsofaffin labarai, domin ni na ƙirkiri labarin kusan shekaru sha bakwai da suka gabata, kuma Allah bai nufa an yi shi ba sai a wannan lokacin. Amma da yake shi labari ne da yake da daidai da kowanne lokaci ba wani abu ne na abin da ya faru a yanzu za a iya gama shi ba, nan da shekaru arba’in idan aka fito da labarin ‘Muhalli’ zai iya gamsar da mutanen lokacin. Saboda fim ne da yake koyar da tarbiyya da wasu abubuwa da mutum zai gujewa a rayuwa don kada ya faɗa cikin wani hadari.
Sannan kaga ko daga sunan labarin ma za ka ga duk dan adam yana da buƙatar ‘Muhalli’ a rayuwarsa , to wannan dalilin ne ya sa muka zaɓi mu sakawa fim ɗin sunan ‘Muhalli’ tun a wancan lokacin kuma Allah bai yi za a fitar da shi ba kuma wani bai yi tunanin zai yi fim ya fitar da shi da wannan sunan ba , duk da sunan ba shi da wahala. Kuma ga shi sai a wannan lokacin Allah ya kaddara za a yi shi kuma ga shi ana ci gaba da gudanar da aikin sa.”
Ya ƙara da cewa, “Kuma ka ga a yanzu an samu ci gaban zamani don haka a yanzu aikin fim ya fi sauƙi fiye da lokacin baya don haka wasu abubuwan da muke samar da su a cikin aikin ya fi mana sauki ma fiye da lokacin baya, don haka aikin fim muna yin sa ne cikin tsari da kuma ci gaban zamani ba kamar a baya ba, don haka in sha Allahu su ma masu kallo za su ga sauyi da ci gaban zamani kuma za su gamsu da aikin mu. In sha Allahu kwalliya za ta biya kudin sabulu.”
Shi ma jarumi a cikin fim ɗin Ahmad Bifa ya ce, “To shi wannan fim ɗin na ‘Muhalli’, an shirya shi ne a kan wasu aminan juna da suka taso a unguwa ɗaya sai ɗaya ya samu arziki ɗaya kuma yana a matsayin talaka, kuma ni na fito a matsayin talaka, shi kuma abokina ya kasance mai arziki, amma duk da haka bai guje ni ba ya nemi na zo na zauna tare da shi, kuma gaskiya saboda saƙon da yake cikin fim ɗin ko da aka bani labarin na karanta sai na ji na gamsu da zan fito a matsayin da aka ba ni. Kuma gaskiya rol ɗin ya yi tasiri a gare ni, ya sa na fahimci duk inda za ka tafi ya kamata ka waiwaya baya ka duba abokan ka da kuka taso tare, ka taimakawa masu buƙatar taimako a cikin su, kuma ka yi duk yadda za ka yi don kada zumunci ya yanke , saboda ka samu abin duniya ka rabu da mutanen da ka taso da su tun daga kuruciya. Don haka wannan fim ɗin ya saka mini abubuwa da yawa da na fahimci yadda rayuwa take shi ya sa nake iya yi na don na bayar da tawa gudunmawar, don haka jama’a za su ga irin ɗimbin darasin da yake cikin fim ɗin, domin shi saƙon sa a bayyane yake , don haka za a ga yadda fim cin ya bambanta da sauran waɗanda aka saba kallo.”
Ita ma jaruma Fa’iza Abdullahi wadda ta kasance a cikin fim ɗin ‘Muhalli’, Ta shaida mana cewar “Gaskiya wannan aikin fim ɗin ya burge ni. Duk da dai a cikin aikin fim ina taka rol na mara kunya marar tsoro da sauran rol kala-kala amma gaskiya, wannan rol ɗin da aka bani na fito a masifaffiyar mace na fi jin dadin sa kuma ya burge ni, don na nuna rashin mutunci yadda raina take so, don haka nake son wannan fim ɗin na ‘Muhalli’, don ka ga na fito a matsayin matar aure amma marar mutunci ga kuma rashin tarbiyya. To gaskiya rol ɗin ya yi mini daɗi sosai yadda nake so, don ka ga na fito a matsayin matar mai kuɗi sosai amma kuma ba na girmama shi, don haka wannan darasi ne ga masu irin wannan hali.”
A taƙaice dai za a iya cewa fim ɗin ‘Muhalli’ ya zo da sabon salon da su masu fim ɗin suke ganin na su ya bambanta da sauran waɗanda ake yi a baya da kuma yanzu, don haka suke ganin fim ɗin ‘Muhalli’ zai iya canza akalar harkar fim a masana’antar finafinai ta Kannywood daga nan zuwa lokuta masu zuwa.
