Majalisar Wakilai na neman a raba ofishin Antoni-Janar da na Ministan Shari’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Wakilan Nijeriya ta shirya neman tabbatar da ƙudirin da zai buƙaci a raba ofisoshin Antoni-Janar na ƙasa da kuma na ministan shari’a.

Haka ma ofisoshin Antoni-Janar na jihohi za a raba su da na kwamishinan shari’a kowacce jiha.

Ƴan majalisa Mansur Soro (PDP) da Oluwole daga (PDP) daga jihohin Bauchi da Osun suka ɗauki nauyin gabatar da ƙudirin ƙarƙashin shugaban kwamitin nazarin doka kuma mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu.

Ƙudirin na neman gyara ga sashe na 150 na dokar ƙasa ta 1999 ta hanyar ƙara sakin layi ɗaya da zai bada damar hakan a mataki na ƙasa da kuma na jiha.

A lokacin da ya ke jawabi game da batun, ɗan majalisa Soroya ce hakan na zuwa ne a ƙoƙarinsu na ƙara inganta adalci ga manyan laifuka da bin doka da oda a jihohi da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya ce ministan shari’a da Gwamnatin Tarayya da kwamishinoni za su riƙa bada shawarwarin shari’a ga muƙarraban gwamnati da sanya ido kan adalci a tsare-tsare.

By Babaji