
Daga RABIU SANUSI
Tsoffin ɗaliban makarantar sakandire ta Pilot dake Daura a Jihar Katsina, ajin shekarar 2010 sun gudanar da taron ɗabbaƙa zumunci da taimakon juna.
Taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na farfajiyar makarantar dake Ganga a Garin Daura, ya samu halartar da yawa daga cikin mambobin ɗaliban.
Da yake jawabi, ɗaya daga cikin shugabannin riƙon ƙwarya, Yusuf Muhammad Sadau ya bayyana irin jin daɗinsa bisa yadda aka samu amsa wannan katin gayyata cikin ƙanƙanin lokaci da aka bayar.
Sadau ya ce sanin kowa ne cewa babu al’ummar dake samun cigaba sai sun samu haɗin kai.
Ya ce lallai wannan makaranta na cikin halin da ya kamata ace an kawo mata ɗauki don maido da martabarta zuwa mataki nagaba.
”Muna miƙa sakonmu ga Shugabancin wannan makaranta cewa in sha Allahu nan gaba kadan wannan Kungiya zata mika wani sako ga wannan makaranta dan taimaka mata.
Wasu daga cikin shugabanin rikon da suka hada da Usman Alhassan, Aliyu Shitu da Nazifi Rabe Zango sun bayar da shawarwari daban-daban da za su kawo ma tafiyar ci-gaba.
Shugaban makarantar wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Malam Bala Muhammad ya ce gaskiya irin wannan taro yana da kyau a irin wannan taro a rinƙa duba ga irin yanayin da abokan karatun su.
Malam Bala Muhammad ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin jihar Katsina na mayar da makarantar zuwa ta kwana wanda a halin yanzu shiri ya yi nisa.
Daga karshe ya yi ma dukkan wanɗanda suka halarci taron fatan alkhairi da kuma koma wa gida lafiya.
