Gwamnatin Katsina za ta kashe biliyan N1 a gyaran KTTV

Spread the love
Dakta Bala Salisu Zango

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Bayanin ya fito ne daga bakin kwamishinan yaɗa labarai da aladu na jihar, Dakta Bala Salisu zango a yayin bikin ƙarshen shekara da gidan talabijin na KTTV ya shirya wa ma’aikatansa.

Bala zango ya ce gwamnati ta sanya kuɗin ne a kasafin kuɗinta na shekarar 2025 da Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya sanya hannu.

Kwamishinan ya yaba da jagorancin babban Manajan gidan talabijin ɗin, Abba Zayyan kan gagarumin ci-gaba da aka samu a wajan shirye-shirye da kula da jin daɗin ma’aikatan KTTV.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan da su tashi tsaye wajan ciyar da KTTV gaba tare da bai wa babban manajan haɗin kai ga harkokin ci-gaba .

A nasa jawabin, Abba Zayyan ya yaba wa ma’aikatansa bisa irin haɗin kai da suke ba shi tun lokacin da ya karɓi jagorancinsu.

Ya ce duk nasarar da ya samu sai da goyon bayan su, ya na mai alkawarin cigaba da kyakkyawan jagoranci da kamanta adalci.

Da ya ke tsokaci wajan bikin, shugaban ƴan jarida ta ƙasa reshen jihar Katsina, Kwamared Tukur Hassan Ɗan Ali ya yi kira yayi ga ɗaukacin ma’aikatan gidan gwamnatin na KTTV da su zage dantse wajan ɗaukaka gidan talabijin ɗin ta yadda za ta yi gogayya da takwarorinta na jihohi.

By Babaji