An shiga fargaba kan ƙaratowar wa’adin Mele Kyari a matsayin shugaban NNPC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ana ƙara nuna damuwa dangane da ƙarewar wa’adin Babban Jami’in Kamfanin Man Fetur ta Nijeriya, Mele Kyari, da kuma yiwuwar naɗa sabon shugaban da zai jagoranci harkokin katafaren ɓangaren man.

Wasu masu sa ido a masana’antar na ganin cewa shugaban na NNPC, wanda zai cika shekaru 60 a ranar 8 ga Janairu, 2025, na iya ficewa daga kamfanin mai na ƙasa, abin da ke ƙara nuna damuwa game da makomar shugabancin kamfanin nan gaba.

Wannan ya zo ne a yayin da wasu mutane suka bayyana cewa, ana sa ran wa’adin Kyari zai ƙare a shekarar 2027, bisa bin sashe na 59 (2) na dokar masana’antar man fetur ta 2021 wanda ya bayyana cewa, “Kundin Tsarin Mulkin Hukumar NNPC ƙayyade daidai da Dokar Kamfanoni.

A watan Yulin 2022, NNPC ta sauya sheƙa daga kamfanin gwamnati zuwa wani kamfani mai iyaka, kuma Kyari ya koma daga matsayin Manajan Darakta zuwa Babban Jami’in Rukunin.

Kyari, wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa a watan Yulin shekarar 2019, tsohon ma’aikataci ne a harkar man fetur, inda ya yi aiki a NNPC tsawon shekaru 32.

Sama da shekaru biyar da yayi yana aiki a matsayin shugaban NNPC kuma shi ne mafi daɗewa da kowane shugaba ya shafe a ofis a masana’antar man Nijeriya tun bayan dawowar dimokraɗiyyar ƙasar a 1999.

Tun da aka kafa hukumar ta NNPC a shekarar 1977, tana da manajoji 19, biyu ne kacal daga cikinsu (Farfesa Funsho Kupolokun (Ondo, 2003-2007), Augustine O. Oniwon (Kogi, 2010-2012) daga Kudu maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Haka kuma Kyari yana ɗaya daga cikin naɗe-naɗen muƙƙmai tare da Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya, Gbenga Komolafe, wanda Shugaba Bola Tinubu ya gada wanda har yanzu ba a kore shi ba.

Kwanan nan, wani farfesa a fannin aikin jarida ɗan ƙasar Amurka, Farooƙ Kperogi, ya yi kira ga Tinubu ya karɓe ragamar mulkin ƙasar ta NNPC.

By ukarofi