Lakurawa sun kashe ‘yan sanda biyu da sace shanu sama da 200 a Kebbi

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ƙungiyar Lakurawa ne sun kashe ‘yan sanda biyu tare da sace shanu sama da 200 a ƙauyen Natsini da ke ƙaramar hukumar Argungu a Jihar Kebbi.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren Alhamis.

Majiyoyi daga ƙauyen sun bayyana cewa ‘yan sandan na tsare ne a wani shingen bincike a kan titin Augie/Kangiwa lokacin da ‘yan bindigar fiye da 50, ɗauke da babura, suka kai musu hari suka kashe biyu daga cikinsu. Daga nan kuma suka nufi inda shanun suke a ƙauyen Natsini, wanda yake kusan kilomita biyar daga garin Argungu, suka kwashe su.

Wani mazaunin yankin, Abubakar Augie, ya ce shanun mallakar wani babban ma’aikacin gwamnati mai suna Lawali Black ne. Ya ƙara da cewa, “Lakurawa sun kai mutum fiye da 50 ɗauke da babura. Bayan sun samu nasarar kashe ‘yan sandan da ke shingen, sai suka je gonar inda ake kiwon shanun suka tafi da su.”

Shugaban ƙaramar hukumar, Aliyu Gulma, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an fara gudanar da taron tsaro kan wannan al’amari. Ya ce gwamnatin jiha ta bayar da umarnin a bi ‘yan bindigar tare da ƙoƙarin dawo da shanun da aka sace.

Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, bai samu damar magana da manema labarai ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

By ukarofi