Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya rantsar da ƙarin Kwamishinoni guda bakwai 7 da za su kara taimakawa majalisar Zartarwar Jihar Kano kaimi wajen sauke nauyin da Allah ya ɗora masu.
Gwamnan ya kuma tabbatar da rantsuwar kama aikin wasu daga cikin mutane 13 a matsayin manyan masu bashi shawarwari a gwamnatinsa tare da manyan sakatarori guda 6
Gwamnan ya kuma bayyana cewa kamar yadda aka sani a zuwan gwamnatinsa, sun gudanar da ayyuka daban-daban a ɓangarorin Ilimi, Lafiya, Noma, Tallafa wa mata da matasa da jari don dogaro da kai.
Sauran sun haɗa da samar da ruwan sha, Tsaro da samar da Hanyoyi da sauran su.
”Zan yi amfani da wannan dama domin jan hankalin dukkan wanda muka bai wa muƙami da su sani cewa duk abin da muke yi ba ya wuce ganin yadda zamu kawo ma jihar Kano ci-gaba ta hanyoyi da yawa.”
Wanɗanda suka samu muƙaman sun haɗa da Alhaji Ibrahim Waiya, Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai; Hon Shehu Wada Sagagi Kwamishinan Ma’aikatar Ciniki da sanya Hannun-jari; Hon Nura Ma’aji, Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Kadarorin gwamnati.
Sauran Kwamishinonin sun hadar da Hon. Ɗan Maraya, Ma’aikatar Kudi; Dakta Gaddafi, Ma’aikatar Samar Da Hasken Wutar lantarki; Dakta Ɗahiru Hashim a matsayin kwamishinan Muhalli; sai Hon Abdulƙadir Abdussalam tsohon ma’aji a matsayin Kwamishinan Raya Karkara.
A nasa jawabin, tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar kuma sabon kwamishinan Ma’aikatar Cinikayyar da Zuba hannun-jari, Shehu Wada Sagagi, ya yi godiya a madadin sauran kwamishinonin tare da tabbatar wa mai girma Abba Kabir cewa za su yi bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da an ciyar da gwamnatin gaba.
