Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana ƙudurin shi na ɗaukar matakin daya kamata ga dukkan kwamishinan daya kawo masu wasa a gwamnatin su.
Alhaji Abba Kabir ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar zartarwa karo na 23 da ake gudanarwa a duk lokacin da ya kamata dan bayyana ma al’ummar Jihar Kano dukkan abinda yakamata su samu da kuma sani game da gwamnatin da suka zaɓa.
”Yanzu, kuma a wannan lokaci da muke ciki ba zamu lamunci dukkan wani shashanci ba, dan haka dukkan kwamishinan da ya kawo mana wargi ko wasa zamu ɗauki matakin da ya kamata akan shi.
”Zamu yi amfani da wannan dama dan ƙara jan hankalin ku sababbin kwamishinoni da ku tsaya ku haɗa kan ku waɗanda kuka samu dan aiki tare da zai ɗaga martabar Jihar Kano.”
Yayin zaman majalisar zartarwar gwamna Abba Kabir ya kuma bayyana wasu shirye-shiryen da gwamnatin shi zata gabatar nan bada jimawa ba, kama daga gobe idan Allah ya kai mu.
Wasu daga cikin ayyukan da za su gabata dan inganta rayuwar jama’ar Kano sun haɗa da biyan wasu daga cikin ‘yan fansho da zai gudana a gobe Alhamis na Naira Bilyan Biyar dan tabbatar da alƙawarin da suka ɗauka yayin yaƙin neman zaɓe.
Haka zalika gwamna ya kuma bayyana shirin gwamnatin su na bada kayan makaranta kyauta ga ɗaliban ajin farko zuwa sati mai zuwa idan Allah ya kaimu.
”Muna kuma tabbatar da shirye-shiryen mu masu yawa da muke dasu nan da Kwanaki Kaɗan masu zuwa na wannan sabuwar shekarar na bai wa waɗanda ruwa yayi masu ɓarna da gwamnatin tarayya ta bai wa kowace jiha.
”Muna kuma bada tabbacin nan da watanni uku masu zuwa zamu gina matsakaitan gidaje da zasu laƙume kimanin naira bilya 10 ga waɗanda ruwa ya yi masu ɓarna in Allah ya yarda.
Gwamna Kanon yace wasu daga cikin abubuwan da suka faru a cikin kwanaki kaɗan na ƙarshen shekara da ta gabata sun haɗa da dawowar ɗaliban Jihar Kano daga Ƙasar Indiya bisa ƙaro ilimin digiri na biyu da gwamnati ta tura su.
Sannan ya ƙara da batun sanya ma Kasafin kuɗin shekarar da aka shigo ta 2025 kusan sama da bilyan 700 dan ganin an samu cigaba a ɓangarori daban-daban.
Haka kuma gwamnan ya kuma Ƙara miƙa saƙon shi na godiya ga majalisar dokokin Jihar Kano bisa haɗin kai da suke baiwa ofishin shi na fatan samun nasarar shi a gwamnatance.
”Idan kuna biye damu kan abinda yake faruwa yanzu akwai batun ƙara wasu kwamishinoni guda bakwai dan ƙara kawo al’ummar Jihar Kano kusa da Gwamnati.
