Kalmomin Nijeriya 20 sun shiga ƙamus na Oxford

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fitaccen ƙamus ɗin Turancin na duniya, wato Oxford, ya faɗaɗa kansa, inda ya shigar da ƙarin wasu kalmomi guda 20 da ake amfani da su a Nijeriya.

Sabbin kalmomin da aka shigar sun haɗa da shahararrun kalmomi kamar “japa,” “agero,” “eba,” “419,” da “abi,” da sauransu.

Waɗannan kalmomi, waɗanda suka yi ƙaurin suna a cikin rayuwar yau da kullum na ’yan Nijeriya, sun nuna tasirin Turancin Pidgin, da kalaman al’adun Nijeriya da ke ƙara samun karɓuwa a duniya.

Musamman ma, wasu kalmomin, kamar su “japa” da “jand,” suna bayyana matsayin sunaye ne a cikin ƙamus.

An kuma samar da bayanai don taimaka wa waɗanda ba ‘yan Nijeriya ba wajen sanin asalin ma’anar kalmomin.

Wani mai ba da shawara kan Turancin Ingilishi na Nijeriya ga ƙamus na Turanci na Oxford, Kingsley Ugwuanyi, ya sanar da sabuntawa akan LinkedIn ranar Talata.

Ya nuna jin daɗinsa kan rawar da ya taka wajen tsara kalmomin da kuma faɗar yadda ake furta su.

Ga cikakken jerin kalmomin Nijeriya da aka saka a cikin ƙamus na Oɗford:1. 419
2. abi
3. adire
4. agbero
5. area boy
6. cross-carpet
7. cross-carpeting
8. eba
9. Edo
10. gele
11. jand (noun, verb)
12. janded (adjective)
13. Japa (noun, verb)
14. Kanuri
15. Kobo
16. Naija
17. suya
18. Yahoo
19. yahoo boy
20. Yarn Dust

By ukarofi