Karatu ta yanar gizo ne makomar neman ilimi – Shugaban NOUN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida ta Nijeriya (NOUN), Farfesa Olufemi Peters, ya bayyana cewa tsarin karatu daga gida (ODL) ya kasance makomar ilimi a duniya.

Hakan dai ya zo ne kamar yadda jami’ar ta yi wa sabbin ɗalibai 23,344 rajista waɗanda suka yi rajistar karatun digiri daban-daban da na digirin digirgir.

Peters ya bayyana haka ne a wajen bikin kammala karatun digiri karo na 27 a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, 2025, inda ya tarɓi ɗaliban da suka shiga jami’ar.

Bikin wanda aka gudanar a kusan kuma a cibiyoyin karatu na NOUN a duk faɗin ƙasar, ya kuma shaida rantsar da sabbin ɗalibai.

Peters ya nanata ƙudurin NOUN na kawo sauyi a fannin ilimi a Nijeriya, yana mai bayyana ODL a matsayin makomar ilimi, musamman a cikin duniyar da ke ƙara ƙaimi ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire na dijital da kuma buƙatar samar da tsarin ilmantarwa.

By ukarofi