Za mu fitar da Afrika daga ƙangin talauci, inji Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Talata ya ce, shugabannin Afirka sun ci gaba da jajircewa wajen fitar da al’ummarsu daga ƙangin talauci da gina tattalin arzikinsu a matakan da suka dace.

Tinubu, wanda ya kasance babban baƙo na musamman, ya bayyana haka ne a wajen rantsar da shugaba John Mahama a birnin Accra na ƙasar Ghana.

“Ba mu da wani abin da za mu tabbatar wa kowa sai kanmu. Mun samu hanya mai muhimmanci don samun nasarar mu. Za mu fitar da al’ummarmu daga ƙangin talauci, mu gina tattalin arziki mai ɗorewa.

“A yau, na zo nan ba kawai a matsayina na shugaban Nijeriya ba ne, har da matsayina na ɗan Afirka mai cikakken goyon baya ga Ghana da mutanenta,” inji Tinubu.

Ya ce rantsar da Mahama abin alfahari ne ga al’ummar Ghana, da ɗaukacin nahiyar, da kuma ‘yan ƙasashen waje.

“Muna bikin Dimokuradiyyar Afirka a yau yayin da Ghana da al’ummarta masu kauna ke bikin miƙa mulki daga gwamnatin dimokuraɗiyya zuwa waccan.

“Wannan lokacin ya wuce alamar wani muhimmin ci gaba a cikin juyin halittar al’ummar dimokuraɗiyyar Ghana.

“Yana haifar da tambayar ko Ghana da Afirka za su iya gudanar da ayyukan dimokiraɗiyya da fa’ida. Ghana ta amsa wannan tambayar da kyau.”

Ya ce kamar yadda Ghana ta samu kwarin gwiwa da ƙarfi daga Kwame Nkrumah da da yawa daga cikin shugabanninta da suka shuɗe, haka nan Nijeriya ta samu ƙwarin gwiwa daga shugabannin da suka kafa ta waɗanda ba wai kawai sun yi gwagwarmayar kwato mata ‘yancin kai ba, har ma sun mutunta dangantakar ƙut-da-ƙut ke tsakanin ƙasashen biyu.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa sabuwar gwamnati a ƙarƙashin jagorancin Mahama, za ta yi aiki tare da Nijeriya don ƙarfafa danƙon zumunci mai ƙarfi, wanda zai haifar da wadata ga jama’ar ƙasashen. Ba ni da tantama gwamnatinku za ta kawo sauyi mai kyau da ci gaba.

“Haka hawan ku kan karagar mulki ya kamata kuma ya zama wani sabon ci gaba mai cike da kuzari wajen neman haɗewar yankin da ci gaba.

“Tare da mayar da hankali, za mu iya magance matsalolin mutanenmu: talauci, rashin aikin yi na matasa, rashin zaman lafiya, tashe-tashen hankula, da sauran matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban da muke so,” inji Shugaban.

By ukarofi