Gwamnan Kano ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin aikin hajji

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta rage kuɗin aikin hajjin 2025 don bai wa mahajjata damar gudanar da ibada.

Gwamnan ya ce, kiran ya zama wajibi bisa la’akari da ƙalubalen tattalin arziki da ‘yan ƙasar ke fuskanta.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Sanusi Bature, ya fitar ranar Talata a Kano.

Yusuf ya bayyana haka ne a wani taron da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar ta shirya, domin mayar da kuɗaɗen da hukumomin ƙasar Saudiyya suka aika sakamakon wani tsaiko da aka samu a lokacin aikin Hajjin shekarar 2023.

Ya kuma yaba wa gwamnatin Saudiyya bisa wannan karimcin, sannan kuma ya yi alƙawarin aika takardar godiya ta musamman ga masarautar Saudiyya ta ofishin jakadancinta da ke Kano.

Da yake yaba wa Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) bisa taka tsantsan da mayar da kuɗaɗen da ta yi a kan kari, Yusuf ya yaba mata bisa nasarar gudanar da aikin hajjin 2024, ya kuma buƙace ta da ta ci gaba da gudanar da aikin cikin inganci.

Yusuf, wanda ya ziyarci Saudiyya kuma ya gudanar da aikin Umrah a makonnin da suka gabata, ya ce jihar ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2025, don gano wuraren da ke bukatar kara shiga tsakani.

Sanarwar ta kuma ruwaito Aminu Abdulsalam mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban tawagar alhazai ta jihar Kano a shekarar 2024 yana yaba wa gwamnan bisa goyon bayan da yake baiwa hukumar alhazai.

Darakta Janar na hukumar, Laminu Danbaffa, ya ce an mayar da Naira miliyan 375.

By ukarofi