Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Adadin bashin da ake bin Nijeriya zai kai Naira Tiriliyan 187.79 a bana, yayin da ƙasar ke fama da hauhawar farashin kaya da faɗuwar darajar Naira.
A cewar wani rahoto na baya-bayan nan na Cardinalstone, wani kamfani na zuba jari da bincike wanda ya nuna cewa bashin ƙasar zai kai Naira tiriliyan 153.04 a ƙarshen shekarar 2024.
Wannan tarin basussuka a cewar rahoton, yana da nasaba ne da bayar da lamuni na cikin gida na dala (dala biliyan 900.00), ciyo rance akai-akai ta asusun baitul malin Nijeriya (NTB) da kuma komawar ƙasar a kasuwar hada-hadar kuɗi ta Euro dala biliyan 2.20.
“Mun kiyasta bashin gwamnati zai kai Naira tiriliyan 187.79 a shekarar 2025. Hauhawar bashin gwamnati ya ƙara nuna damuwa game da ɗorewarsa,” inji manazartan a cikin rahoton nasu mai taken ‘Matsi’.
Basusukan da ake bin Nijeriya ya ƙaru matuƙa a cikin ‘yan kwanakin nan, inda ya haura daga Naira Tiriliyan 49.85 kafin zaɓen 2023 zuwa Naira Tiriliyan 134.30 a ƙarshen rubu’in farkon shekarar 2024.
