Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kasafin kuɗi da sake fasalin haraji, Taiwo Oyedele, ya yi watsi da ikirarin cewa kwamitin bai tuntuɓi gwamnonin Nijeriya ba.
Gabatar da ƙudurorin da gwamnatin Bola Tinubu ta yi ya haifar da cece-kuce musamman a arewacin ƙasar inda ƙungiyar gwamnonin Arewa, da ƙungiyar dattawan Arewa, da sauran su suka nuna rashin amincewarsu da ƙudirin.
Dokar da aka gabatar na neman sake fasalin tsarin tattara haraji da gudanarwa na ƙasar, tare da ba da damar kafa tsarin haraji mai inganci da daidaito, ya haɗa da ƙudirin dokar harajin Nijeriya na 2024, da dokar kula da haraji, da dokar kafa hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta Nijeriya, da kuma dokar kafa hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta haɗin gwiwa.
Tun da farko dai wani dattijon ƙasa kuma ɗan siyasar Arewa Buba Galadima ya yi ikirarin cewa kwamitin harajin ya gaza tuntuɓar gwamnoni, inda ya ƙara da cewa ƙudurorin sun yi daidai da jihohin Ogun da Legas, inda ya ce kwamitin da Oyedele ke jagoranta ta kasa haɗuwa da kowani gwamna sai na Legas.
Da yake magana a gidan talabijin na Arise a ranar Lahadi, Oyedele ya caccaki zargin Galadima, inda ya bayyana cewa shugabannin gwamnatocin jihohin sun soke tarurruka huɗu da aka shirya yi.
Ya ce, “Muna da cibiyoyin gwamnati sama da 20 da ke wakilta. Muna da kamfanoni masu zaman kansu, ko masana’anta ne, ko mata ne a cikin kasuwanci. Muna da ɗalibai 45 daga jami’o’i 22 a faɗin Nijeriya.
“Bugu da ƙari, mun yi hulɗa sosai da gwamnonin. Na je dandalin gwamnoni. Mun rubuta kuma mun so ganawa da gwamnoni shida, ɗaya daga kowane yanki na yankuna shida. Har zuwa wannan lokacin, gwamnan jihar Legas ne kawai muka iya gani.
“ɗayan gwamnan da ya yi maraba da mu shi ne gwamnan jihar Kaduna. Kuma bayan duk wannan aiki, mun amince da rana ɗaya, a wannan ranar bai sami damar halarta ba. Mataimakiyar gwamna ne ta karɓi baƙuncin mu. Ba zan ambaci sunayen sauran gwamnonin ba, amma zan iya gasgatawa idan ina buƙata. Ba su da lokacinmu.
