Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Alamu masu ƙarfi sun bayyana cewa farashin man fetur na iya ƙara faɗuwa a shekarar 2025.
ƙwararru a harkar mai, waɗanda suka zanta da jaridar The Sun, sun bayyana cewa man fetur wanda a halin yanzu ake sayar da shi tsakanin N900 zuwa N950 a yawancin gidajen mai, zai iya ƙara fazuwa zuwa ƙasa da Naira 500 kan kowace lita.
A cewar masu ruwa da tsaki a harkar mai, yuwuwar faɗuwar farashin man fetur a shekarar 2025 ya ta’allaƙa ne kan wani ɓangare mai ƙarfi da ke ƙarƙashin tsarin gwamnatin tarayya.
A cewar ’yan kasuwar, wasu dalilan da suka haddasa faɗuwar farashin sun haɗa da tsayayyen manufofin musayar kuɗaɗen waje, gasar farashin, manufofin Naira na ɗanyen man fetur da kuma zuwan matatun mai na Fatakwal, Warri, da Dangote. Sun kuma tabbatar da cewa matatun sun sayar da kayayyakinsu a kasuwannin cikin gida kuma su karɓar kuɗin su a Naira zai taimaka wajen faɗuwar farashin.
A watan Yulin da ya gabata ne majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da sayar da ɗanyen man fetur ga matatun man ƙasar a kuɗin naira.
Ban da wannan kuma akwai sake dawo da ayyukan matatun mai na zamani, waɗanda a halin yanzu sun yi tasiri a ɓangaren da ke ƙarƙashin ruwa, kuma sun kammala shirin ƙara tace man fetur a bargarsu na kayayyakinsu baya ga dizal wanda a halin yanzu shi ne layin kayayyakinsu.
Wannan na zuwa ne a yayin da ake ci da man fetur a Nijeriya a kullum ya kai kusan lita miliyan 40 da ake nomawa a cikin gida. A bisa bayanan da manyan motocin dakon kaya suka fitar daga Hukumar Kula Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), Matatar Dangote ta ba da gudunmawar kusan lita miliyan bakwai yayin da kamfanin NNPC ke sarrafa lita miliyan 1.2, wanda ya kawo adadin zuwa lita miliyan 8.2.
Matatun mai na zamani sun ɗaga tuta saboda kawai suna samar da dizal a yanzu. A halin yanzu ƙasar tana da matatun mai na zamani guda 25 masu lasisi amma biyar ne ke aiki.
Hakan na nufin cewa kashi 20.5 cikin 100 na buƙatar man fetur din kasar nan ne ake biya ta hanyar tacewa a cikin gida, yayin da sauran kashi 79.5 ko kuma lita miliyan 31.8 ake shigo da su daga ƙasashen waje.
