Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamitin Raba Kuɗaɗen Asusun Tarayya (FAAC) ya raba jimillar Naira Tiriliyan 5.38 ga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja tsakanin watan Janairu zuwa Disamba 2024.
Wannan adadin ya nuna ƙarin kusan Naira Tiriliyan 1.46 fiye da Naira Tiriliyan 3.92 da Jihohi da Abuja suka samu a shekarar da ta gabata.
Jihohin sun samu jimillar Naira biliyan 412.09 a watan Janairu; Naira biliyan 406.96 a watan Fabrairu; Naira biliyan 454.70 a watan Maris da kuma Naira biliyan 428.24 a watan Afrilu.
Jimlar Naira biliyan 463.04 ta samu a watan Mayu; Naira biliyan 365.81 (mafi ƙarancin kasafi na shekara) a watan Yuni kafin a kai Naira biliyan 461.98 a watan Yuli da kuma Naira biliyan 473.48 a watan Agusta.
Sauran sun kasance kamar haka: Satumba: Naira biliyan 422.86; Oktoba: Naira biliyan 453.72; Nuwamba: Naira biliyan 490.70 da Disamba: Naira biliyan 549.79 wanda ya kasance mafi girman kaso na shekarar.
Waɗannan rabo sun yi tasiri ta hanyar ayyukan kuɗaɗen shiga gabaɗaya da ƙa’idojin da FAAC ke amfani da su don ƙididdige rabon.
Idan aka kwatanta, kason na 2023 ya yi kaɗan, inda ya kai Naira biliyan 396.21 a watan Janairu, kuma ya yi kasa da Naira biliyan 259.50 a watan Afrilu.
Rabon ya nuna ingantacciyar hanyar samun kuɗaɗen shiga a shekarar 2024, sakamakon cire tallafin mai, da ƙaruwar sayar da mai da kuma samun ƙarin kuɗin shiga daga sassan da ba na mai ba, gami da haraji.
A cikin jihohin, Delta ta samu mafi girman kaso a watan Maris na 2024 da Naira biliyan 62.7, sai Jihar Ribas da Naira Biliyan 41.7, sai Jihar Akwa Ibom da Naira Biliyan 41.6. Jihohin da ake haƙo mai suna cin gajiyar wannan ƙa’idar ne, wanda ke tabbatar da cewa wani ɓangare na kuɗaɗen shigar mai na tafiya kai tsaye zuwa jihohin Neja Delta.
Ana sa ran ƙaruwar kason zai taimaka wa gwamnatocin jihohi wajen inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da kuma ci gaban tattalin arziki. Masu ruwa da tsaki sun buƙaci kashe kuɗi don tabbatar da inganta rayuwar ‘yan ƙasa.
ƙididdigar kason jihohin ta hanyar rabon kuɗaɗen ya nuna cewa Delta, Ribas, Akwa Ibom, Legas da Bayelsa ne suka samu kaso mafi tsoka.
Delta ta samu jimillar biliyan N485; Ribas biliyan N384; Akwa Ibom, N338bn; Legas, biliyan N321 da Bayelsa, biliyan N293.
Sauran manyan kuɗaɗen shiga da aka ware sune: Kano, biliyan N166; Edo, biliyan N124; Ondo, biliyan N122; Anambra, biliyan N115 da Oyo biliyan N113.
Tare da jimillar Naira tiriliyan 5.38 da aka ware a shekarar 2024, masana na da kwarin gwiwar ci gaba da samun ƙaruwar kuɗaɗen shiga zuwa shekarar 2025.
