’Yan kasuwa za su fara dakon fetur daga matatar Warri a Fabrairu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masu sayar da man fetur sun fara lodin man dizal da kalanzir daga matatar man fetur ta Warri.

Dillalan sun tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Juma’a, yayin da suka buƙaci kamfanin da aka gyara kwanan nan, da ya fara tace man fetur zuwa watan Fabrairun 2025.

WRPC, ƙarƙashin jagorancin Kamfanin Mai na Nujeriya, ya fara aiki ne a ranar 30 ga Disamba, 2024, bayan da Babban Jami’in Kamfanin na NNPC, Mele Kyari, ya sanar da komawarsa aiki a wani rangaɗin da ya kai matatar.

Da yake zantawa da ɗaya daga cikin manema labarai a ranar Juma’a a matatar man, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwan mai mai zaman kanta ta Nijeriya reshen jihar Delta, Harry Okenini, ya ce duk da cewa kamfanin na aiki amma ba ya aiki ɗari bisa ɗari.

Sai dai ya yi nuni da cewa ‘yan kasuwa sun fara lodin man dizal da kananzir.

“A yanzu haka, babu fetur. Don haka, ba mu fara lodin fetur ba. Muna fatan za mu fara loda man fetur nan ba da jimawa ba. Za mu iya tabbatar muku da cewa matatar tana aiki amma ba a kashi 100 ba. Kuma IPMAN, reshen Warri na jiran samar da man fetur don mu fara lodi.

“A yanzu dai dizal da Kananzir ne kawai ake tacewa.

“Da fatan zuwa watan Fabrairu, muna sa ran fitowar iskar gas da man fetur da sauran kayayyakin. Ya zuwa yanzu, sashin sayar da kayayyaki yana lodi ne kawai na dizal da kalanzir,” inji shi.

Shima da yake zantawa da manema labarai a matatar, Shugaban Kamfanin NUPENG, Israel Omokere, ya bayyana cewa matatar tana aiki.

Ya ce, “Da fatan za a fara tace fetur. Muna loda kananzir da dizal ne kaɗai a yanzu.” 

By ukarofi