Tinubu ya sha alwashin kammala layin dogo na Fatakwal zuwa Maiduguri

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta kammala aikin layin dogo na Gabas da ya haɗa Fatakwal zuwa Maiduguri.

Tinubu ya bayar da wannan tabbacin ne a wata tattaunawa da ya yi da shugabannin Kudu maso Gabas a Enugu a ziyarar da ya kai jihar ranar Asabar, Bayo Onanuga, wanda mai magana da yawunsa ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.

Shugaban ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatin sa za ta tallafa wa ci gaban yankin Anambara a matsayin wani gagarumin tanadin makamashi.

An yi kiyasin cewa yankin yana ɗauke da ganga biliyan ɗaya na mai da kuma na gas biliyan 30.

Shugaba Tinubu ya yaba wa Gwamna Peter Mbah kan tsarin cigaba da falsafa bayan ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa Enugu da sauran jihohin ƙasar nan a ƙoƙarinsu na samar da ci gaba.

Daga cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar akwai makarantar GTC Smart Green; Titin New Haɓen/Bisalla, Cibiyar Taro ta Duniya, Cibiyar Kula da Umurni da Kulawa, da motocin sintiri 150 sanye da kyamarorin sa ido.

Shugaban ya kuma gudanar da aikin ƙaddamar da wasu fitattun ayyuka daga gidan gwamnatin jihar Enugu.

A wajen ƙaddamar da cibiyar kwamandoji, shugaban ya ce zuba jari a fannin tsaro zai kawo ci gaba cikin sauri a ƙasar.

By ukarofi