Gwamnatin Katsina za ta sake ɗaukar malamai aiki a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta shirya ɗaukar malaman makarantun firamare da sakandare a faɗin jihar.

Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya (SUBEB), Dakta Kabir Magaji Gafiya ya faɗi haka a wajan taron masu-ruwa-da-tsaki a harkokin ilimi da aka shirya a jihar.

Taron, wanda ya gudana a garin Katsina ya samu halartar masu-ruwa-da-tsaki akan harkokin ilimi daga dukkan hukumomi da kananan hukumomi 34 a jihar.

Dakta Kabir ya ce maƙasudin shirya taron shine a tattauna da masu-ruwa-da-tsaki tare da bayar da shawarwari kan yadda za a samar da wani sabon sashin da zai kula da ingancin karatu a makarantun firamare da na sakandare da ke jihar (Education Service Unit).

Ya bayyana cewa za a buɗe wata sabuwar manhaja ta tattara bayanai domin inganta harkokin koyo da koyarwa a makarantun jihar watau EMIS APPLICATION a turance.

Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ya kuma jiddada ƙudirin Gwamna Dikko Raɗɗa na inganta harkar ilimi a jihar.

Taron na wuni ɗaya ya samu halartar masana da suka gabatar da ƙasidu daban-daban akan yadda za a haɓaka harkokin ilmi da kuma mahimmancin samar da da sahihin alƙaluma da za a inganta ilimi a jihar.

A shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki malamai fiye da dubu 8 waɗanda ke koyarwa a makarantun firamare da sakandare a jihar.

By ukarofi