CITAD ta ƙaddamar da shirin WiDEF don kawar da giɓin da ke akwai a fasahar intanet a Arewa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Cibiyar Fasahar sadarwa da cigaban al’umma ta CITAD ta ƙaddamar da shirin samarwa da mata aikin yi ta hanyar Intanet, wato Women in the Digital Economy Fund (WiDEF), wanda shiri ne da niyyar kawar da rashirin aiki na ƙasa da ƙasa a Arewacin Nijeriya.

Shirin mai mai taken: Fuskantar ƙalubalen da ke addabar mata da samar masu da damarmaki a arewacin Nijeriya.
(AGENDA-WIN),” wanda ya fara a watan Disamba 2024 kuma zai gudana ne cikin shekaru biyu a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi da Yobe sai kuma Legas da Ribas a matsayin jihohin da za a kimanta tasirin shirin.

Da ta ke wa manema labarai Ƙarin haske a ofishin CITAD da ke Kano,ranar Juma’a Manajan shirin WiDEF, Zainab Aminu, ta bayyana cewa, shirin ƙawance ne da aka samu tallafi daga USAID da Bill & Melinda Gates Foundation, tare da haɗin gwiwa daga kamfanoni na duniya kamar Microsoft, Reliance Foundation, CARE, Global Digital Inclusion Partnership, da GSMA Foundation.

Ta ƙara da cewa, shirin na da niyyar kawar da duk wani tarnaƙi da ke hana mata da ‘yan mata shiga harkokin sadarwa ta intanet da kuma bunƙasa tattalin arzikinsu da inganta rayuwar mata a Nijeriya.

“Koma baya da ake samu na rashin fasahar intanet na ci gaba da zama barazana, domin ko a rahoton Hukumar Sadarwa ta Duniya (ITU) na baya-baya nan ya nuna cewa akwai mata 244 miliyan da ba su da damar shiga intanet fiye da maza a duniya. A Najeriya, hukumar ƙididdiga ta Ƙasa ta nuna cewa mata sune koma baya da kashi 20% na ayyukan fasaha, wanda hakan ke nuna buƙatar da ke akwai na ɗaukar matakin gaggawa.

“Babban burin WiDEF shi ne na toshe duk wani banbance banbance da ke akwai tare da samar masu fasahar intanet ta hanyar sadaukar da mata da ‘yan mata su zama ƙwararru a fagen sadarwa da kuma ƙirƙirar damarmakin kasuwancin intanet”

Zainab ta ƙara da cewa, shirin zai kawo fa’ida a tattalin arziki da kuma a zamantakewa ta yadda zai ciyar da mata gaba,

“Lallai samar wa da mata aikin yi kamar korar talauci ne, ta yadda cigaban al’umma da ƙirƙire-ƙirƙire za su haɓaka”.

Sannan ta yi kira ga gwamnatoci da ma’aikatu masu zaman kansu da ƙungiyoyin fararen hula da su zo a haɗa ƙarfi da ƙarfe don kawar da bambancin da ke akwai a fannin Fasahar nan ta sadarwa da cigaban tattalin arziki da fasahohin zamani ga ‘yan Mata.

By ukarofi