Muna bin manyan mutane bashin biliyan N300 na mallakar filayen Abuja – Wike

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike a daren Lahadi ya ce basussukan Takardun Mallakar Filaye (C of O) da hukumar birnin ke bin manyan masu kuɗi sun haura Naira Biliyan 300.

Wike ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a gidansa da ke Life Camp, Abuja.

Ministan ya kuma bayyana cewa, tsantsar kuɗaɗen shiga da ya ke samu ya ƙaru daga kusan biliyan N9 a lokacin da ya hau kan karagar mulki a watan Agustan 2023 zuwa matsakaicin biliyan 25 duk wata.

Ya ce, babban birnin ƙasar ya samar da sama da biliyan N40bn a watan Disambar 2024.

Ya danganta ƙaruwar kuɗaɗen shiga da tara kuɗaɗen haya da kuma biyan kuɗaɗen takardun mallakar filaye (C of O) ta hanyar rabon filaye. Ministan ya ce, FCT na biyan albashi har naira biliyan 13 duk wata.

Wike ya ce: “Ba ma samun biliyan N13 daga harajin ɓAT da kashi 1% daga Gwamnatin Tarayya. Don haka, dole ne mu ƙara haɓaka samar da harajin cikin gida don samun damar biyan sabon mafi ƙarancin albashi.

“Kamar yadda a lokacin da na zo, muna samar da kusan biliyan N9 zuwa biliyan N10. A yau cikin ikon Allah ba a samun ƙasa da biliyan N25 a wata.

“Hakan ya kasance ne saboda tarin kuɗin shigarmu. Hasali ma, a watan da ya gabata, mun samu damar samar da kusan Naira biliyan 40 da ‘yan kai. ƙaddamar da kuɗaɗen shiga don samun damar aiwatar da abubuwan more rayuwa

“Dole ne mu tsawwala a kan haraji domin idan ba a biya haraji ba ta yaya za mu samu ci gaba?” ya tambaya.

By ukarofi