Wata tanka ɗauke da fetur ta yi bindiga a yankin Ugwu Onyeama, ƙaramar hukumar Udi, Jihar Enugu, a ranar Asabar, inda ta hallaka mutane da dama. Lamarin ya faru ne kusan kilomita kaɗan daga cikin garin Enugu, da misalin ƙarfe 12:30 na rana.
Rahotanni daga wurin sun bayyana cewa gobarar ta yi matuƙar ɓarna, inda ta ƙone motoci da dama tare da salwantar da rayukan mutane da yawa. Duk da cewa wasu rahotanni sun bayyana adadin wadanda suka mutu ya haura 20, babu wata tabbatacciyar sanarwa daga hukumomin da suka dace dangane da lamarin.
Shaidu daga wurin sun ce tsananin wutar gobarar ya hana ƙoƙarin ceto waɗanda ke cikin motoci da suka yi karo da ibtila’in. Mutanen da suka mutu a hatsarin sun ƙone har ba a iya ganewa, inda ake zargin su ne fasinjojin da ke cikin motocin da suka kama da wuta.
A halin yanzu, ‘yan sanda da hukumar kiyaye haɗɗura ba su tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ko sanadin fashewar ba, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
