Kwangilar Mambilla: Abubuwan da Obasanjo da Buhari suka faɗa a kotun Paris

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A makon da ya gabata ne tsofaffin shugabannin Nijeriya, Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari suka faɗa wa Kotun Sasanci ta ‘International Chamber of Commerce Court of Arbitration’ dake Paris a Faransa cewa Gwamnatin Tarayya ta bada kwangilar Dala biliyan 6 ga Kamfanin Sunrise Power a Jihar Taraba don gudanar da aikin Wutar lantarkin Mambilla.

Obasanjo da Buhari sun kare Nijeriya ne a ƙarar sasancin, wanda kamfanin da wanda ya samar da shi, Cif Leno Adesanya sukai shigar bisa zargin Gwamnatin Nijeriya da karya dokar kwangila.

Kamfanin Sunrise ya ce ya na neman a biya shi kuɗaɗen da ya kashe da waɗanda aka biya a harkokin doka.

Tsoffin shugabannin ƙasar sun roƙi kotun da ta yi watsi da yarjejeniyar ta 2003, wadda Adesanya da kamfaninsa suka gina ƙararsu a kai sobada takardar ba karɓaɓɓiya ba ce kasancewar tsohon Ministan Lantarki, Dakta Olu Agunleye ya sanya hannu ne kwana ɗaya bayan Majalisar Zartarwa ta ƙi amincewa da bai wa kamfanin kwangilar.

A halin yanzu, ana gudanar da shari’a akan Ogunleye a Abuja kan amfani da bayanan bogi, rashin biyayya ga umarnin shugaban ƙasa da rashawa game da kwangilar.

EFCC ta zarge shi ne da bada kwangilar gina Tashar lantarki ta Ruwa mai nauyin megawat 3,960 a Mambilla ga Sunrise ba tare da tsare-tsaren kasafi ko samun amincewa ba.

Bayanan da Obasanjo da Buhari suka bayar sun samu goyon bayan Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na ƙasa, Lateef Fagbemi; magajinsa, Malam Abubakar Malami; Tsohon Ministan Lantarki, Babatunde Fashola da kuma Tsohon Ministan Albarkatun Ruwa, Injiniya Suleiman Adamu.

Haka kuma, jaridar The Nation ta ruwaito cewa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na ƙasa, Mista Mike Aondoakaa ya halarci Paris, wanda ya riƙe muƙamin ne a zamanin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua. Saidai, ba a san wani ɓangare ya je karewa ba daga cikin ɓangarorin biyu.

Sannan, Kamfanin ko Leno Adesanya ba su gabatar da wani shaida ba a yayin taron manema labarai don ji ta bakinsu.

Wata majiya ta ce Obasanjo da Buhari sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun kare martabar Nijeriya.

By Babaji