
Daga BELLO A. BABAJI
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya ce shahararren jagoran ƴan ta’adda, Bello Turji ya bayyana ƙudirinsa na son ya miƙa wuya sakamakon ƙarfin dakarun tsaro.
Ya ce jami’an sojoji ba za su amince da buƙatar ba, ya na mai cewa za su cigaba da farautarsa har sai sun cim masa a maɓoyarsa.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a yayin hira da gidan talabijin ɗin channels a ranar Juma’a, inda ya ƙara da cewa tuni ɗan ta’addar ya sallami da dama daga cikin waɗanda ke ƙarƙashinsa.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji sun yi nasarar kashe da dama daga cikin manyan ƴan ta’addan da ke aiki tare da Turji ciki har da mataimakinsa, Aminu Kanawa.
Babban Hafsan Tsaron ya kuma yi alwashin cewa ba za a taɓa ƙyale wanda ya ke da hannu a kisan mutanen da ba su da laifi ya tafi a banza ba.
“Mu na son ganin bayan kowaye. Duk wanda ya kashe, shi ma a kashe shi. Mutane irinsa bai kamata a bar su a raye ba”, inji Janar Musa.
