Gwamnan Kano ya kuma nemi malamai su rama wa kura aniyarta
Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya da su haɗa kai guri guda domin samun zaman lafiya baki ɗaya.
Gwamna Abba Kabir ya yi kiran ne a yayin taron bikin maulidin Sheik Ibrahim inyasi da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata cikin birnin Kano.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin shi za ta cigaba da haɗa kai da ƙungiyoyin addinai domin samar da tsaro ga al’ummar Jihar Kano da inganta rayuwar matasa maza da mata ta hanyar samar musu da ayyukan yi domin dogaro da Kai.
“Muna amfani da damar wannan taro domin Ƙara kira ga malaman addini na kowane ɓangare da su ƙara ƙaimi wajen Kira ga mabiyan su domin tabbatar da zaman lafiya a wannan jiha dama Ƙasa baki ɗaya.
“Kowa ya sani irin tasirin da malaman mu suke da shi tun a baya wajen kawo sauyi da tunatarwa musamman yadda yake a karantarwar Alƙur’ani da faɗar manzannin Allah maɗaukaka.”
Alhaji Abba Kabir ya Kuma jinjina ma yaba da malaman wajen yadda suke faɗakarwa ga al’umma a wannan gari da Allah yayi ma albarka ta fuska mai yawa.
Kazalika gwamna ya Ƙara kira ga al’umma na ciki da wajen ƙasar nan da su taimaka wajen cigaba da samar da Addu’o’in zaman lafiya dan tattalin arziki ya ƙara bunƙasa a jiha da ƙasa baki ɗaya.
“Muna ƙara kira ga jama’ar mu da su ƙara ƙaimi wajen cigaba da biyayya koyarwar addini bisa koyarwar Manzo S.A.W.
Wakilin mu ya kalato mana cewa wannan taro na maulidi da aka gudanar ya samu halartar manyan malamai,masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen ƙasar Najeriya.
A yayin taron an dai baje kolin basira tare da karantowa daga cikin littafi mai tsarki watau Alƙur’ani da haddisan manzon tsira SAW.
Shima a nashi jawabin mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi ya buƙaci jama’a su ƙara haɗa kawunan su domin samun cigaba.
Sarkin ya kuma buƙaci waɗanda suka zo wannan taro da su Ƙara cigaba da abinda yakamata dan samar da zaman Lafiya a Jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya.
Khalifa Muhammad Sanusi ya kuma yi fatan komawa lafiya ga dukkan wanda ya samu halartar wannan wajen mai albarka, inda kuma ya jinjina manyan baƙi da sauran malaman da suka bada gudunmuwa a wannan taro.
