Wani abin fashewa ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a mahaƙar ma’adanai a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani abin fashewa a wajen haƙar ma’adanai a Sabon Pegi dake ƙaramar hukumar Mashegun a Jihar Neja ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da raunata wasu.

Lamarin ya auku ne da ranar Lahadi a lokacin da masu haƙar ma’adanai suka fara gudanar da ayyukansu a yankin.

Kawo yanzu ba a san musabbabin faruwar al’amarin ba, saidai ana alaƙanta hakan da rashin kula da kayan aiki masu fashewa daga kamfanonin masu haƙar ma’adanai, kamar yadda mazauna garin Sabon Pegi suka bayyana.

Rahotanni daga garin sun bayyana cewa an gano gawa guda huɗu daga wajen da abin ya faru.

Hukumomi na cigaba da gudanar da bincike don bada ba’asi kan cikakken bayani akan al’amarin.

Haka kuma gwamnatin jihar ko jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ta musamman game faruwar al’amarin ba.

By Babaji