Raɗɗa ya raba wa ‘yan takarar ƙananan hukumomi na APC a Katsina tuta

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya raba wa yan takarar kujerar shugabannin ƙananan hukumomi 34 tutar APC a jihar.

Bikin wanda ya gudana a ƙaramar hukumar Ingawa ya sami halartar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje da sauran manyan ya’yan jam’iyyar.

A jawabin sa bayan ya ƙarɓi mutane 40.000 da suka sauya sheka zuwa APC, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin babban jami’i ya a ƙasar.

Ya ce, APC ce kawai ke bin dimukraɗiya wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar.

Kun ga dai yadda ya’yan jam’iyun adawa ke tururuwa zuwa jam’iyar mu ta APC wanda ya nuna itace kaɗai jam’iyar da ke gudanar da harkokin jam’iyyar kan turba ta dimukraɗiya.

Ya yabawa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan yadda ya kawo wa ƙasar bunƙasa da walwalan alumma.

A nasa jawabin gwamna Dikko Raɗɗa ya ce jam’iyyar APC tana nan,daram, kuma bata tsoron ayi zaɓe a kowane lokaci domin ita za tayi nasara.

By ukarofi