Daga USMAN KAROFI
‘Yan ta’adda da ake zargin Boko Haram/ISWAP ne sun kai farmaki a sansanin soja na Malam-Fatori, hedikwatar ƙaramar hukumar Abadam da ke Jihar Borno, inda suka kashe kwamandan soja, manyan jami’ai biyu, da sojoji 17. Wannan hari ya faru ne a ranar Juma’a, 24 ga Janairu, 2025, bayan wasu hare-haren da suka yi wa al’umma a Gadan Gari da ke ƙaramar hukumar Bama, inda suka kashe mutane 20 a ranar Laraba.
Malam-Fatori na yankin Arewacin Jihar Borno kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar, yayin da Bama ke tsakiyar jihar. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga sansanin sojan Malam-Fatori ɗauke da manyan bindigogi da motoci ƙirar gun truck, inda suka yi ɓarna tsawon sa’o’i kafin su ƙwace sansanin 149 Battalion.
Wata majiya ta tabbatar da cewa an kone gine-gine da dama da kuma motocin aikin sojoji a yayin harin. Haka kuma, an samu raunuka a jikin wasu sojoji da dama, yayin da har yanzu ba a san adadin waɗanda suka ɓata ba. Kwamandan rundunar, wasu jami’ai biyu, ciki har da likitan sansanin, sun mutu a wannan harin.
A ɗaya ɓangaren, a harin da aka kai Gadan Gari, wani ɗan ƙungiyar tsaro ta Civilian Joint Task Force, Modu Ari, ya bayyana cewa maharan sun isa yankin da misalin ƙarfe 11:00 na safe, inda suka buɗe wuta kan manoman kifi. Mustapha Kachallah, wani mazaunin yankin, ya ce ɗansa na cikin waɗanda aka kashe, kuma an riga an binne gawarwakin mutane fiye da 15 a garin.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun hare-hare a Jihar Borno tun daga watan Nuwamba na bara, inda aka kashe sama da manoma 40 a Dumba da ke ƙaramar hukumar Kukawa. Al’amarin ya zama ƙalubale ga gwamnatin tarayya da sojojin Najeriya wajen dawo da zaman lafiya a yankin, yayin da ake ƙoƙarin maido da ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu na asali.
