Waiya ya yi alƙawarin samar da dokar ‘Yancin Samun Bayanai a Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Kwamishinan bayanai na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana ƙudurinsa na tabbatar da samar da dokar ‘Yancin samun bayanai’ (FOI) a Kano domin ƙarfafa dimukraɗiya da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a gwamnati. Waiya, wanda ya taɓa shugabantar ƙungiyar Kano Civil Society Forum, ya ce hakan zai taimaka wajen inganta haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma.

A wata hira da aka yi da shi, Kwamishinan ya bayyana cewa za a ƙirƙiro wani dandali mai suna “Kano Citizens Platform” da zai ba al’umma damar bayyana ra’ayoyinsu game da ayyukan gwamnati da kuma karɓar martani daga hukumomin gwamnati. Ya ƙara da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, shi kansa zai ƙaddamar da wannan dandali domin tattaunawa da ‘yan jihar kai tsaye.

Kwamared Waiya ya kuma bayyana cewa suna da shiri na wayar da kan shugabannin ƙananan hukumomi da kuma ƙungiyoyin al’umma akan yadda za su sa ido da kuma kula da ayyukan raya ƙasa. Ya ce a baya sun ƙirƙiro kundin bayanai na ƙungiyoyi sama da 4,400 a jihar, inda kowace ƙaramar hukuma ke da wakilai 100. Wannan zai ƙara musu fahimtar hanyoyin zamani na sa ido da inganta ayyukan gwamnati.

Dangane da dokar FOI, Waiya ya bayyana cewa yawancin ma’aikatu da hukumomin gwamnati ba su fahimci dokar sosai ba, wanda hakan ke haifar da matsaloli wajen samun bayanai daga gwamnati. Ya ce yana da shiri na wayar da kan jami’an gwamnati game da dokar, tare da tabbatar da cewa dukkan ma’aikatun gwamnati suna bin ƙa’idojin samar da bayanai ga al’umma.

A ƙarshe, Waiya ya jaddada cewa gwamna Abba Yusuf yana kan turbar tabbatar da gaskiya da adalci, kuma yana son ganin gwamnati ta kasance mai buɗe kofa ga al’umma. Ya ce Kano, wacce ke matsayin cibiyar kasuwanci a Afirka, za ta ci gaba da kasancewa jagaba wajen tabbatar da cigaban ƙasa da inganta sunan jihar a idon duniya.

By ukarofi