Ƙungiyar ɗalibai ta bai wa Gwamnatin Tarayya kwana 14 ta gyara hanyar Numan-Jalingo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS), ta bayyana hanyar Numan zuwa Jalingo a matsayin turken mutuwa, inda ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako biyu ta sake gina titin.

Shugaban NANS na ƙasa, Mista Lucky Emonefe ya bayyana hakan a ranar Asabar a Jalingo yayin ƙaddamar da Majalisar Zartarwar ƙungiyar reshen Arewa maso Gabas, ya na mai gargaɗin matuƙar gwamnati ta gaza yin aikin hanyar, to za su gudanar da zanga-zanga.

Ya kuma ce matuƙar gwamnati ta ƙi fara aikin hanyar har wa’adin da suka bayar ya ƙare, za su sauya sakatariyar ƙungiyar daga Abuja zuwa Arewa maso Gabas.

Hallau, ya bayyana hanyar a matsayin ɗaya daga cikin munanan hanyoyi a Nijeriya, wadda saboda lalacewarta, ta zama barazana ga rayukan mutane ciki har da ɗalibai.

Haka kuma Emonefe ya yi kira ga Ma’aikatar Ayyuka a mataki na tarayya da ta umarci ɗan kwangilar da aka bai wa aikin gyaran titin ya gaggauta dawo wa aikin don ceto rayukan al’umma.

Daga ƙarshe, ya yaba wa Gwamna Agbu Kefas na jihar kan yadda tsare-tsarensa ke fifita harkokin ɗalibai a jihar, ya na mai bayyana shi a matsayin gwamnan da ya fi kowane gwamna damuwa da harkokin ilimi a Nijeriya.

By Babaji