Tinubu na takaicin fashewar tankar mai akai-akai – Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce Shugaba Tinubu ya yi matuƙar nuna takaicinsa kan yadda ake samun hatsarin fashewar tankokin mai a manyan titina da wuraren al’umma a sassan Nijeriya.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, a lokacin da ya aika saƙon jajensa ga Gwamnatin Jihar Enugu da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a yayin fashewar tankar mai a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Asabar ne aka samu iftila’in fashewar wata tankar mai a yankin Ugwu-Onyeama, ɓangaren babbar titin zuwa Enugu-Onitsha.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen faruwar ire-iren haka a Nijeriya, ya na mai cewa lallai Shugaba Tinubu na cikin takaici da samuwar iftila’in a wurare daban-daban na faɗin ƙasar musamman a Arewa.

Shettima ya kuma jaddada wa al’umma cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta dakatar cigaba da faruwar haka a hanyoyin ƙasar, ya na mai cewa za ta yi aiki da hukumomin da suka dace musamman na kiyaye haɗurra (FRSC) wajen cimma hakan.

Kazalika Mataimakin shugaban ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rayukansu da jajenta wa waɗanda suka jikkata a yayin hatsarin, ya na mai yi musu kyawawan addu’o’i da samun sauƙi raunukan da suka samu cikin lokaci.

By Babaji